• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

by Khalid Idris Doya
3 years ago
pdp

Kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, (PDPCC) ya bukaci hukumar yaki da karya tattalin arzikin kasa da ha’inci (EFCC) da hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) su gaggauta cafke dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan zargin da ake masa na safarar miyagun kwayoyi da yin ruf da ciki da dukiyar jiha.

A wani taron manema labarai da suka yi a yau Lahadi a Abuja, PDP ta ce bayan an kama Tinubun, a hanzarta gurfanar da shi a gaban kuliya kan wadannan zarge-zargen.

Kakakin kwamitin yakin zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Mista Daniel Bwala ya bukaci NDLEA ta nemi cikakken bayani daga Tinubu don ya fayyace bayanai kan dalilan da suka janyo har hukumomi a kasar Amurka suka kwace masa Dala 460,000.

Bwala, kazalika ya yi tir da wata kungiyar da ya ce Tinubu ta kafa, da ya ce kamar kungiya ce ta mayakan sa-kai, sai ya nemi hukumomin tsaro da su cafke da gurfanar da duk wani da ya kasance cikin kungiyar mai suna ‘Jagaban Army’.

Sun Yi zargin cewa an kafa kungiyar ce kawai domin kawo yamutsi da firgici gabanin da yayin zabuka.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

  • 2023: Manyan ‘Yan Takara Na Shafa Wa Juna Kashin Kaji

Ya kara da cewa mambobin jam’iyyar adawa da dama suna fuskantar kalubale da barazana kashi-kashi gabanin zaben 2023.

Wani ma daga cikin masu magana da kwamitin yakin zaben na PDP, Phrank Shaibu, shi ma ya zargi Tinubu da cewa har yanzu yana cikin zargin harkallar kwayoyi.

Kazalika kwamitin ya zargi Tinubu Wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne da yin sama da fadi da dukiyar jihar a lokacin da yake matsayin gwamna.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne bayanai suka karade cewa wata kotu a Amurka ta kwace wasu dalolin Amurka daga asusun Tinubu a yankin arewacin Illinois kan zargin alaka da fataucin kwayoyi.

Sai dai kuma takardun bayanan ba su ba da wasu bayanai ko tabbatar da cewa an yi wa Tinubu shari’a ba, ko kuma yana da alaka da wata kungiyar fataucin kwayoyi.

Takardun sun kuma nuna cewa an yi wannan shari’a ce shekaru 30 da suka gabata.

A cewar bayanan, wannan yanayi ne ya tursasa wa Tinubu sadaukar da kudaden da yawansu ya kai dala 460,000 a daya daga cikin asusun bankunansa 10.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
Da ɗumi-ɗuminsa

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas
Da ɗumi-ɗuminsa

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas

October 22, 2025
Next Post
Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.