Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya lashe mazabarsa ta Arewacin Yobe da gagarumar nasara a zaben majalisun tarayya da na Shugaban kasa wanda ya gudana ranar Asabar a fadin kasar nan.
Da take sanar da sakamakon zaben da misalin 11:30 na daren ranar Lahadi, Baturiyar zaben (Returning Officer), Farfesa Omolola Aduloju, daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gashu’a, a cibiyar tattarawa da sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi shida (6) na Yobe ta Arewa; Bade, Jakusko, Karasuwa, Nguru, Yusufari da Machina, ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda ya samu nasara a zaben.
Ta kara da cewa, a cikin adadin kuri’un da aka yi rijista a kananan hukumomin, kimanin 122136, da yawan kuri’un da aka jefa a zaben 126677, sannan kuma da kuri’u 4541 da suka lalace; jam’iyyar NNPP ta samu kuri’u 7210, sai PDP mai kuri’u 22849, yayin da jam’iyyar APC ta samu adadin kuri’u 91318 a ilahirin kananan hukumomi shida a yankin.
Jami’ar zaben ta bayyana cewa, “Ni Farfesa Omolola, a matsayin Baturiyar zabe a Yobe ta Arewa, wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabarairun 2023, zabe ne da yan takara suka fafata. Kuma bisa dokar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Sanata Ahmed Lawan na jam’iyyar APC shi ne dan takarar da ya zarta abokan takararsa da yawan kuri’u 91318, saboda haka na ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zabe a Yobe ta Arewa.”
Kamar yadda sakamakon ya nuna, Sanata Lawan ya doke abokan takararsa na jam’iyyar PDP, Hon. Ilu Bello Yusufari, wanda ya samu kuri’u 22849, da kuma Hon. Daiyabu Garba Hamza na jam’iyyar NNPP mai kuri’u 7210, da Hon. Sheriff Alhaji Bunu na jam’iyyar ADC mai kuri’u 756.
Bugu da kari, an gudanar da zaben tare da sanar da sakamakon zaben a gaban wakilan yan takara da na jam’iyyu, jami’an tsaro da yan jaridu tare da masu sanya ido, cikin tsanaki da kwanciyar hankali.