Sanata Dino Melaye ya fice daga jam’iyyar PDP a hukumance, saboda ikirarinsa na cewa, jam’iyyar ta gaza wajen fitar da sahihin shugabanci da zai ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da ta shiga na siyasa.
Melaye ya bayyana ficewarsa ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Yuli, a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X (Twitter). A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata, 4 ga watan Yuli kuma aka aika wa shugaban jam’iyyar PDP na Ward 1 a Aiyetoro Gbede, karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, Melaye ya bayyana cewa: “Wannan shawarar ta zama wajibi saboda rashin karfi da kwarin gwiwa da jam’iyyar ke da shi na kubutar da al’ummar Nijeriya daga cikin kunci da suke ci a siyasance”
- Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
- An Yanke Wa Mai Gadi Da Mai Dafa Abinci Hukuncin Kisa Kan Kashe Tsohon Kwamishina A Katsina
Ya kuma kara da cewa, bayan nazari mai zurfi, ba zai iya ci gaba da shiga cikin harkokin jam’iyyar ba, ko kuma ya goyi bayan manufofinta.
Melaye wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben jihar Kogi a 2023, har yanzu bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba a nan gaba. Sai dai rahotanni na nuni da cewa, yana iya sauyawa zuwa jam’iyyar ADC – wata gamayyar jam’iyyar adawa da a baya-bayan nan ta jawo hankalin wasu jiga-jigan masu sauya sheka da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp