A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar.
In ba a manta ba, a ranar 18 ga Maris, 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar. Inda ya ce, “hakan ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin mahukuntan jihar – ɓangarorin zartarwa da na dokokin jihar sun gaza yin aiki tare.
“Ana ɓarnata muhimman kadarorin tattalin arzikin jihar da suka hada da bututun mai, sannan ‘yan Majalisar jihar sun rabu kashi biyu, Mambobi hudu ne kacal ke goyon bayan Gwamna yayin da 27 ke adawa da shi. A irin wannan yanayi, Gwamnan ba zai iya gabatar da wani kudiri na kasafin kudi ga majalisar ba, don ba shi da damar samun kudaden tafiyar da al’amuran jihar Ribas.
“Har ila yau, Kotun koli, a daya daga cikin hukunce-hukuncen da ta yanke a jerin kararrakin da ɓangaren zartarwa da na majalisar dokokin jihar Ribas suka shigar a kan juna, ta ce babu gwamnati a jihar Ribas. A ɓangare na na Shugaban ƙasa, da sauran ’yan Nijeriya masu kishin kasa, mun yi iya ƙoƙarinmu don magance rikicin amma lamarin ya ci tura.
“Don haka, babu wata hanya face in yi amfani da ikon da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya ba ni, don ayyana dokar ta-ɓaci. A matakin farko an dakatar da ofisoshin Gwamna, Mataimakin Gwamna, da zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida. Watanni shida zasu kare yau 17 ga Satumba, 2025.
“Ina godiya ga Majalisar Dokoki ta kasa, wacce bayan ta yi nazari sosai kan dalilan da suka sa aka kafa dokar ta-ɓacin ta dauki matakai nan take, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Ribas”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp