Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya bar shalƙwatar ƙungiyar a Abuja don amsa gayyatar Ƴansanda kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da wasu tuhume-tuhume.
Ajaero, tare da lauyan ƙungiyar, Femi Falana, da manyan shugabannin ƙwadago, sun bar Pascal Bafyau House, shalƙwatar NLC, da misalin karfe 10 na safiyar yau Alhamis.
- Lallai A Hukunta Waɗanda Suka Kai Mamaya Ofishin NLC – TUC
- NLC Ta Bukaci A Dage Sauraron Tuhume-tuhumen Da Ake Yi Wa Shugabanta Zuwa 29 ga Agusta
A martanin da ƙungiyar ta mayar game da wannan lamari, ta umurci mambobinta su shiga yajin aiki na haɗin kai a duk faɗin ƙasar ranar Alhamis yayin da shugaban nasu zai bayyana a gaban rundunar Ƴansandan Nijeriya don amsa tambayoyi.
Zarge-zargen da ake masa sun haɗa da haɗin baki wajen aikata laifi, da ɗaukar nauyin ta’addanci, da cin amanar ƙasa, karya doka da laifukan yanar gizo.