A yanzu wajajen karfe 2.10pm ne Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar da wakilai na musamman da Shugaban kasa, tare da tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso suka kawo ziyarar ta’aziyyar rasuwar fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Tawagar shugaban kasa wanda ministan kudi Wale Edun, da ministan kasafin kuɗi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ne suka wakilci shugaban kasa Bola Tinubu Tinubu da gwamnatin tarayya a wajen wannan ta’aziyyar da ya gudana a Babban Masallacin Marigayin da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi.
Sannan tsohon ministan wasanni Solonmon Dalung shi ma ya zo ta’aziyyar da wasu fitattun mutane ciki har da sanatoci.














