An sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), kusan shekara guda bayan ya fara shugabancin ƙungiyar. An tabbatar da sake zaɓensa a yayin zaman taron shekara-shekara karo na 65 na Shugabannin Ƙasashen ECOWAS, da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya da ke Abuja a ranar Lahadi.
A cikin jawabinsa na buɗe taron, Shugaba Tinubu ya yi kira ga ƙasashen ECOWAS su ƙara kuɗaɗen da suke warewa don yaƙar ta’addanci a yankin. Ya jaddada cewa domin rundunar ECOWAS ta ko ta kwana ESF don yaƙar ta’addanci zai buƙaci ƙarfin siyasa mai karfi da kuma kuɗaɗen gudanarwa.
- Shugaban Kwamitin ECOWAS: Sin Ta Taka Muhimmiyar Rawa Ga Ci Gaban Yankunan Yammacin Afirka
- Ecowas Za Ta Kafa Dakarun Ko-ta-kwana Don Yaki Da Ta’addanci
“Dole ne mu tabbatar da cewa mun cika tsammanin da shawarwarin da ministocin tsaro da na kuɗi suka bayar domin magance rashin tsaro da kuma samar da kwanciyar hankali a yankinmu,” inji Shugaba Tinubu.
Ya buƙaci ƙasashe mambobin ƙungiyar su ƙara kuɗaɗen da suke warewa don samar da kayan aikin da ake buƙata don tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.