Sakamakon nasarar gwamnan jihar Kano Abba Gida-Gida wanda kotun kolin Nijeriya ta bayyana cewa shi ne halastaccen gwamna, Hajiya Ruƙayya Ahmad Dikko, ‘Yar uwa ga tsohon shugaban kasa Buhari ta raba Keke NAPPED Da sabon mashin kyauta.
Haka ya biyo bayan wani alƙawari da ta ɗaukarwa kanta na cewa idan Allah ya ba Abba Kabir Yusuf nasara a shari’ar da suke yi tsakanin sa da ɓangaren jam’iyyar APC zata cika wannan alƙawari.
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Abba Kabir Yusuf A Matsayin Zababben Gwamnan Kano
- Shari’ar Kano: Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Abba A Kotun Koli
Hajiya Ruƙayya Ahmad Dikko dai ta kasance ‘yar uwa ta jini ga tsohon shugaba Muhammad Buhari domin da mahaifiyar ta da Alhaji Mamman Daura uwa ɗaya uba ɗaya.
Kamar yadda ta shaidawa wakilinmu cewa wata rana a Kano suna tare da ‘yan uwanta waɗanda su kuma ‘yan APC ne, wata mahawara ta ɓarke a tsakanin su, inda wasu ke cewa Abba Gida-Gida ba zai kai labari ba a wannan shari’a da ake gwabzawa da shi, ita kuma Hajiya Ruƙayya Ahmad Dikko tana da fatan cewa Abba ne zai yi nasara.
Bayan duk wannan cacar baki tsakanin ta da ‘yan uwanta cikin raha da wasa ta yi alƙawarin cewa idan Allah ya ba Abba Gida-Gida nasara zata bada kyautar mashin da Keke NAPPED wanda ta cika wannan alƙawari.
“Hankalina ya tashi matuƙa akan wannan shari’a, na so tafiya Abuja, amma Allah bai sa na samu tikiti ba, sai kawai na dawo Daura domin yin wasu hidimomina, ina Daura akan yanke wannan hukunci, inda Allah ya ba Abba Kabir Yusuf nasara.” Inji ta
A cewar Hajiya Ruƙayya Ahmad Dikko ƙaninta wanda ke bi mata shine ya fara kawo mata labarin hukuncin Kotun Kolin Nijeriya cewa an maida wa Abba Kabir Yusuf kuri’unsa da Kotun farko ta kwace masa, sai kuma ga hukunci na cewa shi ne dai ya yi nasara.
Ta ƙara da cewa nan take na yi Sujaddar godiya ga Allah, kuma bata tsaya ɓata lokaci ba sai wajen masu sayar da mashina a garin Daura, inda ta sayi mashin na hawa akan kuɗi Naira miliyan daya da dubu hamsin da kuma Keke NAPPED miliyan biyu da dubu dari biyu da hamsin, inda nan take ta shiga banki ta tura masu kuɗadan su
“A wajan masu sayar da mashinan na ce samo mani wanda zai baiwa Mashin ɗin, sai aka yi sa a da wani mutum marar karfi kuma masoyin Abba Gida-Gida ne, na bashi mashin nan take, ita kuma NAPPED ɗin daman akwai wata mata mai ‘ya ‘ya bakwai da mijinta ya rasu ya barta, sai nasa aka kirata, na bata wannan NAPPED ɗin ‘ inji Ruƙayya Ahmed
Hajiya Ruƙayya ya ce wannan kyauta ta girgiza wannan mata, wacce ba zato-ba-tsammani ta ga an miƙa mata makullan wannan Keke NAPPED domin ta ci gaba da riƙe marayunta, abin ya yi matuƙar girgiza ta so sai.
Daga ƙarshe dai Hajiya Ruƙayya Ahmad Dikko ta bayyana bayyana jin daɗin ta da wannan nasara ta Abba Gida-Gida tare da cewa yanzu haka akwai wasu alƙawaran akan dai gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida).