• English
  • Business News
Sunday, June 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

by Sani Anwar
6 hours ago
in Labarai
0
Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bayanan da masu ruwa da tsaki suka yi ya nuna cewa, yara kanana a Nijeriya na ci gaba da kamuwa da cutar Sikila, sakamakon rashin gwaje-gwaje da kuma jahilci.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar bikin masu cutar Sikila ta duniya, mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, Mista Alaba Balogun ya bayyana cewa; a halin yanzu kashi 25 na magidanta a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila, sannan kuma a duk shekara kusan jarirai 150,000 ne ke kamuwa da cutar, wanda hakan kuma ke daukar kimanin kashi 8 cikin 100 na mace-macen jariran.

  • Yadda Za A Yaki Ciwon Sikila A Nijeriya Daga Tushe – Hajiya Badiyya
  • Uwargidan Gwamna Ta Jagoranci Tattaki Kan Yaki Da Cutar Sikila A Jihar Zamfara

“Wadanda kuma suka tsira, suna fama da shan wahalhalu iri daban-daban; ciki har da yiwuwar lalacewar wasu daga cikin gabobinsu, shanyewar wani bangare daga jikinsu da kuma karin kamuwa da wasu cututtukan. Rashin jin dadi da walwala da abin da ya shafi tattalin arziki na da matukar yawa, kana hakan na tasiri a kan ilimi, aiki, lafiya, hankali da kuma samun walwala.”

Ciwon Sikila cuta ce mai matukar tsanani, wadda kusan mutane miliyan 100 ke dauke da ita a fadin duniya, wadda ta fi shahara a yankunan kudu da hamadar Sahara. Tana dauke da sama da kashi 50 cikin 100 na mace-macen a tsakanin al’ummar da halittarsu ke dauke da nau’i mafi tsanani (Hb SS), wanda Hukumar Lafiya ta Duniya a yankin Afirka ta fi mayar da hankali a kai. A Nijeriya, cutar na ba da gudunmawa kwarai da gaske wajen kisan yara da kuma su kansu manya.

Bayanan, sun fito ne daga bakin masu ruwa da tsaki da kuma manyan jami’an ma’aikatar lafiya ta tarayya a wata tattaunawa daban-daban da LEADERSHIP, daidai lokacin da Nijeriya ta bi sahun al’ummar duniya a ranar Alhamis, domin bikin ranar Sikila ta duniya.

Labarai Masu Nasaba

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila.

Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta.

Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu.

Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin aure ba tare da fuskantar wata matsala ba, inda aka gano ainahin matsayinsu a lokacin da aka gano yaronsu na karshe na dauke da cutar.

Matar, wadda ta nemi a sakaye sunanta ta ce, “Mun yi gwajin jinsin da ake bukata a yi kafin aurenmu, kamar yadda Coci ta bukata. Kazalika, nawa sakamakon ya nuna cewa, ni AA ce; shi kuma mijina AS, saboda haka; mun yi tsammanin cewa, babu wata matsala; sai ga shi yaranmu na uku an gano yana dauke da cutar, bayan mun kai ziyara asibitoci da dama; aka ce mana yaron SS ne.

Har ila yau, ta bayyana yadda abin ya faru cikin ban tausayi, tana mai nuna cewa; ba don an samu matsala tun a farko wajen yin wannan gwaji ba, da yaron nata bai shiga wannan matsala da ya samu kansa a ciki ba.

“An yi kuskure wajen yi mana namu gwajin, yanzu kuma an bar mu cikin tsanani da wahalar rayuwa”, in ji ta.  

Madam Mary Ukaibe, wata mazauniyar Nyanya a babban birnin tarayya Abuja, ita ma ta bayyana yadda ta samu sakamakon bincikenta na karya. An fada mata cewa; AA ce ita, amma gwajin da aka yi mata kwanan nan ya nuna cewa AS ce.

“Allah ya taimake ni, mijina AA ne. Amma da a ce shi ma AS ne, dukkanin mu ba mu sani ba, da za mu buge ne da haihuwar ‘ya’ya masu dauke da wannan cuta ta Sikila mai ban tsoro”, in ji ta.

Ko shakka babu, wadannan ma’aurata na daya daga cikin da dama a Nijeriya da ke fuskanta wannan matsala sakamakon kuskure ko gwaji na karya da aka yi musu. 

Dakta Ifeanyi ya shaida wa LEADERSHIP cewa, tsarin yanayin dakunan gwaje-gwajen jini, ya yi matukar tara na bogi da ma’aikatan da ba su cancanta ba da kuma na’urori marasa inganci, wanda hakan ya haifar da karuwar sakamon jinsi na karya, musamman a tsakanin ma’auratan da ke neman gwajin kafin su yi aure.

“Matsalolin da ake samu daga masu yin gwajin na bogi daga cibiyoyi da dakunan gwaje-gwaje, na taimakawa wajen karuwar haihuwar Sikila a Nijeriya. Wannan matsala ta yadu a tsakanin manya da kuma matsakaita, wadanda kan yi gwajin jinsin halittar kafin su yi aure, amma daga karshe; sai su samu sakamakon bogi ko kuma wanda ke dauke da kuskure a ciki”, in ji shi.   

A cewar tasa, an yi kuskuren sanar da ma’aurata da yawa cewa; sun dace da jinsi, daga nan sai su kai ga yin aure, sai kuma daga bisani a gano cewa; ashe abin ba haka yake ba, watakila bayan sun fara haihuwar ‘ya’ya masu ciwon Sikilar.

Shugaban AMLSN ya ce, wannan ba wai ya takaita kadai ga dakunan gwaje-gwaje masu zaman kansu ba ne, har ma da kafatanin cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, wadanda ba a tantance ba tare da na’urorin da su ma ba a tantance su ba da na jabu da kuma rashin sa ido yadda ya kamata. 

“Ni da kaina na shiga shagunan kwanan nan, don samo kayan aiki, kuma na gano cewa; yawancin samfuran da ke cikin kasuwa na bogi ne. Idan masanin harkar kamar ni, za a iya ba ni na bogi, idan ba na lura sosai ba, ina kuma ga wadanda ba su kware sun san harkar yadda ya kamata ba?”, in ji Dakta Ifeanyi.

Har ila yau, ya yi kira ga hukumomi, musamman kungiyar kimiyyar lafiya ta Nijeriya (MLSCN), da su dauki matakin gaggawa kan daidaita wadannan al’amura tare da tabbatar ganin cewa; ana aiwatar da bin ka’idoji da dukkanin tsare-tsaren da suka kamata.

A cewarsa, dole ne dukkan masana kimiyyar gwaje-gwajen lafiya a fadin tarayyar Nijeriya, su hada karfi da karfe wajen yaki da matsalar sayar da wadannan kayayyaki da suka shafi kiwon lafiya na bogi, wanda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar barazana ga lafiyar al’umma baki-daya.

Lokacin da LEADERSHIP ta tuntubi cibiyar MLSCN, kan kokarin da take yi na dakile wannan al’amari yayin gwaje-gwaje, ta dage cewa; sai an gabatar da takarda a hukumance kafin ta yi magana kan al’amarin. 

Dakta Ifeanyi ya kuma bukaci kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) da cibiyoyin addini da sarakunan gargajiya, da su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma, kan illolin da ke tattare da auren da za a iya kamuwa da wannan cuta ta Sikila.

Yayin da yake amincewa da ci gaban da aka samu wajen tilasta yin gwaje-gwaje kafin a kai ga yin aure ya ce; ana ci gaba da samun raguwar yaduwar cutar a duk shekara.  

“Dole ne mu sake gina al’ummarmu, musamman ta hanyar wayar da kan jama’a game da kimiyya da fasaha da kuma ingantaccen tsarin gwaje-gwajen da ya kamata kowa ya yi”, in ji shi.

A nasa bangaren, mataimakin daraktan sashen kula da gwaje-gwaje a babban asibitin kasa na Abuja, Anthony Ilegogie ya gargadi ‘yan Nijeriya kan dogaro da dakunan da ba su da inganta ko na bogi, domin yin wannan gwaje-gwaje na kawayar halittar Dan’adam, yana mai jaddada cewa; yanayin halittar mutum ba ya canzawa, sannan kuma bai kamata bayan an yi gwaji na gaskiya a sake komawa ya ce za a sake yin wani ba.

A yayin da yake magana kan batun kura-kuren da ake samu dangane da sakamakon gwajin kwayar halittar, Ilegogie ya fayyace cewa; irin wannan matsala na faruwa ne sakamakon rashin horar da ma’aikata da rashin kayan aiki a dakunan gwaje-gwajen da ake da su.  

 “Mutane iri daban-daban, kan shiga wannan harka ko kasuwanci na harkar gwaje-gwajen jini, inda a karshe bayan mara lafiya ya fada hannunsu, sai su buge da ba shi sakamako na karya ko mara kyau”, kamar yadda Ilegogie ya yi gargadi.  

Sannan ya kuma kara da cewa, hanyoyin gwaji na zamani a halin yanzu, sun banbanta da wadanda ake amfani da su a da, domin kuwa yanzun an dogara ne da ingantattun na’urori na zamani da fasahohi, wadanda ke bayar da sakamakon da ake bukata daidai-wadaida. 

LEADERSHIP ta gano cewa, Nijeriya ce kasa mafi dauke da wannan cuta a duk fadin duniya, inda kashi 25 cikin 100 na manya ke dauke da kwayar cutar Sikila tare kuma da kamuwar jarirai kusan 150,000 a duk shekara, wanda hakan ke nuni da cewa; kusan kashi takwas cikin 100 na mace-macen jarirai a kasar na afkuwa.

A cewar mashawarciya ta musamman kan cutar Sikila ga ministan lafiya ta kasa, Farfesa Obiageli Nnodu, a halin yanzu kimanin ‘yan Nijeriya miliyan hudu ne ke dauke da wannan cuta ta Sikila.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: SikilaYara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

Next Post

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Related

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 
Labarai

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

4 hours ago
Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo
Labarai

Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

6 hours ago
Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa
Labarai

Jirgin Alhazai Na Farko Ya Iso Jihar Jigawa

7 hours ago
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100
Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

10 hours ago
Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki
Manyan Labarai

Tinubu Ya Isa Saint Lucia Domin Ziyarar Aiki

12 hours ago
Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25
Labarai

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

1 day ago
Next Post
Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar

Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar

June 29, 2025
Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta

June 29, 2025
2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

June 29, 2025
Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya

Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya

June 29, 2025
Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa

Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa

June 29, 2025
Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

Xi Ya Yi Kira Ga Mazauna Wani Kauye Dake Xizang Da Su Rike ‘Yan Uwantakar Kabila

June 29, 2025
Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

Zaben 2027 Yaƙi Ne Tsakanin Talakawa Da Masu Mulki – Sanata Kaita 

June 29, 2025
Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

June 29, 2025
Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto

June 29, 2025
Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo

June 29, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.