Sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin bai-daya (UBEC), Dr. Hamid Boboye, ya bayyana cewa Nijeriya na bukatar karin makarantu 20,000 da kuma ajujuwa 907,769 domin samun guraban da dalibai ‘yan Makaranta za su tsuguna.
Boboye ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata yayin da yake karin haske ga Babban Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman da Karamin Ministan, Dokta Yusuf Sununu.
Ya bayyana cewa, rashin isassun ajujuwa da ma’aikata, su ne manyan kalubalen da hukumar ke fuskanta a kokarinta na tabbatar da samun ingantaccen ilimi a fadin kasa baki daya.
Anasa jawabin, Farfesa Mamman, ya ce, ma’aikatar ilimi a karkashinsa za ta ba da fifiko ga ilimin bai-daya a fadin kasar.
Mamman ya kuma jaddada cewa, bangaren ilimin bai-daya shi ne bangare mafi muhimmanci a fannin ilimi wanda dole ne a inganta shi yadda ya kamata domin samun nasarori da saukin fahimtar karatu a sauran matakai na gaba a fannin ilimi da kuma samun ci gaban kasa baki daya.
Ya yi kira ga daukacin jihohin tarayyar Nijeriya da su kara himma a bangaren ilimin bai-daya domin kara habaka ilimi a kasar nan.