• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yara Mata Miliyan 370 Ke Fuskantar Cin Zarafi Da Fyade A Duniya –UNICEF

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Zarafi

Wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar, ya bayyana cewa daya daga cikin kowadanne yara mata 8 a duniya suna fuskantar hadarin cin zarafi da fyade. Daya daga cikin matan 5 kuma suna fuskantar irin wannan barazana ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani, wanda adadinsu ya kai miliyan 650.

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UINCEF ya ce, yara mata miliyan 370 ke fuskantar cin zarafi ko kuma fyade kafin su cika shekaru 18 da haihuwa a fadin duniya.

  • Hadin Gurasa Na Zamani
  • Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron AIPPI Na Duniya Na 2024

Rahoton na UNICEF ya kara da cewa adadin cin zarafin yara mata na ci gaba da fadada a sassan duniya, inda yara mata miliyan 79 wanda ya yi daidai da kaso 22 ke fuskantar cin zarafi a kasashen nahiyar Afirka da ke Kudancin Sahara, kafin cikar haihuwarsu shekaru 18.

Sai kuma kasashen da ke Gabashi da kuma Gabas maso Kudancin Asiya, da suke da kaso 8 da adadinsu ya kai yara mata miliyan 75 ne ke fuskantar cin zarafin.

Yara mata miliyan 73 a tsakiyar Asiya da kuma Kudancinta ke fuskantar irin wannan cin zarafi, kafin cikarsu shekaru 18 da haihuwa, inda kason ya kai 9.

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Tarayyar Turai da kuma Arewacin Amurka na da kaso 14 da adadin su ya kai miliyan 68 na yara mata da ke fuskantar irin wannan kalubale, a cewar UNICEF.

Yara mata miliyan 45 ne a yankin Latin Amurka da Caribbean, sai kuma yara mata miliyan 29 a Arewacin Afirka da Yammacin Asiya, da kuma yara mata miliyan 6 a yankin Oceania, inda suke da kaso 18, 15 da kuma kaso 34 na yara mata da ke fuskantar cin zarafi da kuma fyade.

Fatima Usman, daya ce daga cikin iyaye wacce ‘yarta ta taba fuskantar irin wannan cin zarafi a Nijeriya. Ta ce ta ran ta yana kuna sosai a duk lokacin da ta tuna da wannan al’amarin

Dakta Hauwa Babura, daya ce daga cikin mata masu fafutakar kare ‘yancin yara mata a Nijeriya, ta kuma jaddada kididdigar rahoton da UNICEF, ta fitar.

A hirarsa da Muryar Amurka, Isa Sanusi, wanda shi ne Babban Daraktan Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International a Nijeriya, ya ce, yara ma na fuskantar yawaitar fyade da cin zarafi a yankunan da ke fuskantar tashe-tashen hankula a Nijeriya.

Masana na ganin daukar matakai masu tsauri ne kadai hanyar da za ta kawo karshen cin zarafin yara a duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga
Kasashen Ketare

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto
Kasashen Ketare

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Kasashen Ketare

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Next Post
Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano

Yadda Muka Dakatar Da Yunkurin Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC - Kungiyar Arewa Ta Tsakiya

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.