• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yara ’Yan Kwadago Da Ke Kasar Amurka Wadda Ke Ikirarin Kare Hakkin Dan Adam

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A karkashin hasken rana mai zafin gaske, wani yaro dan shekaru 7 da haihuwa ya dukufa kan aikin gona.

Wa zai iya alakanta batun da kasar Amurka, wadda ta fi ci gaban tattalin arziki, kuma a kullum ke daukar kanta a matsayin misali wajen kare hakkin bil Adam? Sai dai wani hoton da kungiyar ’yan kwadagon gandayen noma na kasar Amurka ta fitar ta shafin sada zumunta a bara ya tabbatar da cewa, hakan na faruwa dai a wannan kasa.

  • Japan Ba Ta Boye Yunkurinta Na Yin Fito-na-fito Da Kasar Sin Ba

Tuni yau shekaru sama da 100 da suka wuce, aka fara daukar yara ’yan kwadago aiki a mahakar kwal da gandayen noman ganyen tabar sigari da masaku na kasar. Abin bakin ciki shi ne, duk da ci gaban da ’yan Adam suka samu ta fannin wayewar kai cikin shekarun 100 da suka wuce, har yanzu ana yawan samun yara ’yan kwadago a kasar Amurka.

Musamman a fannin aikin noma, yara ’yan kwadago na kasar ta Amurka sun haifar da damuwa idan aka yi la’akari da yanayin da suke ciki. Bisa kididdigar da kungiyar shirin horar da ’yan kwadagon gandayen noma ta kasar Amurka ta yi, an ce, yanzu haka akwai yara ’yan kwadago kimanin dubu 500 a kasar, kuma da yawa daga cikinsu sun fara aiki tun lokacin da suke da shekaru 8 da haihuwa, kuma suna aiki na tsawon sa’o’i 72 a kowane sati.

Har wa yau, yaran sun dade suna aiki a muhallin dake da sinadarai masu guba. Lamarin da ya sa suke yawan kamuwa da cutar sankara. Ban da haka, sabo da yadda suke aiki da na’urorin noma masu nauyi da kuma kaifi, ba tare da samun horon kariya da suka kamata ba, ya sa su kan fuskanci hadari a lokacin aiki.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Rahoton da jaridar “Washington Post” ta samar ya yi nuni da cewa, daga shekarar 2003 zuwa ta 2016, akwai yara ’yan kwadago 452 da suka mutu a kasar, kuma sama da rabinsu suna aiki ne a gandayen noma.

A bara, masana’antu da dama da ke jihar Wisconsin ta arewacin kasar Amurka sun fuskanci matsalar karancin ’yan kwadago. Don taimaka musu daidaita matsalar, majalisar dokokin jihar ta mai da hankalinta kan yara, inda a watan Oktoban bara, majalisar dattawa ta jihar ta zartas da shirin dokar tsawaita lokacin aiki na ’yan kwadago da ba su balaga ba.

A hakika, bisa yarjejeniyar hakkin yara ta MDD, dole ne a kare hakkin yara, amma sakamakon yadda kasar Amurka ta ki amincewa da yarjejeniyar, inda ta zama kasa daya tilo a duniya da ba ta amince da ita ba, ya sa yaran kasar ba su iya samun kariya daga yarjejeniyar.

A watan Yunin shekarar 2002, a yayin babban taron kwadago na kasa da kasa karo na 90 an tabbatar da ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin “ranar hana yara kwadago ta duniya”, don yin kira ga kasa da kasa da su mai da hankali a kan batun yara ’yan kwadago.

Amma yaushe ne za a kai ga mayar da yarantar da ta kamata ga yaran kasar a matsayin “misalin kare hakkin dan Adam?” (Lubabatu Lei)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Ba A Taron Koli Na Kasashen Nahiyar Amurka Mai Cike Da Nuna Bambanci

Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Ba A Taron Koli Na Kasashen Nahiyar Amurka Mai Cike Da Nuna Bambanci

LABARAI MASU NASABA

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.