Gwamnatin Tarayya ta yaba wa Hukumar Yaƙi Da Ƙorafe-ƙorafen Yaɗa Labarai ta Ƙasa (National Media Complaints Commission, NMCC), mai kula da harkokin yaɗa labarai a Nijeriya, kan hukuncin da ta yanke a kan wata jarida dangane da rahoton bogi da ta buga dangane da yarjejeniyar Samoa.
a wata sanarwa da Rabi’u Ibrahim, Mataimaki na Musamman ga Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayar, gwamnatin ta ce, hukuncin ya nuna muhimmancin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da tunatar da ‘yan jarida irin muhimmiyar rawar da suke takawa wajen yin tasiri kan fahimtar jama’a ta hanyar bayar da rahotanni na gaskiya.
- Hadimin Tinubu Ya Raba Kayayyakin Makaranta Ga Daliban Firamare A Kano
- Zargin Ta’addanci A Zamfara: Matawalle Ya Ƙalubalanci Gwamna Dauda Su Yi Rantsuwa Da Alƙur’ani
Haka kuma, ta jaddada cewa dole ne kafafen yaɗa labarai su bi ƙa’idojin aiki don guje wa rahotanni masu cutarwa.
Da take amincewa da ‘yan jarida a matsayin ginshiƙan dimokuraɗiyya, gwamnatin ta yi nuni da cewa, ‘yancin ‘yan jarida yana tafiya ne tare da alhakin bayar da rahotannin gaskiya.
Ta kuma yaba da shawarar NMCC ta cewa, tilas ne jaridar ta bai wa jama’a haƙuri tare da kuma ɗaukar matakan hana faruwar irin wannan lamarin a nan gaba.
Ta ce: “An yi la’akari da kiran da aka yi ga hukumomin Gwamnatin Tarayya da su ƙara fayyace gaskiya, kuma za a ɗauki matakai don ganin an sanar da ‘yan Nijeriya isassun abubuwan da suka shafi jama’a.”
Ta ƙara da cewa, “Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen samar da yanayin da kafafen yaɗa labarai ke bunƙasa tare da ci gaba da bin ƙa’idojin ɗa’a na ma’aikatar.
“Muna kira ga dukkan kafafen watsa labarai da su ci gaba da kiyaye waɗannan ƙa’idoji kuma su yi aiki tare wajen yaɗa sahihan bayanai, waɗanda ke da muhimmanci ga ‘yan ƙasa.”
Gwamnati ta yi fatan wannan hukunci zai zama wani ma’auni na hazaƙar aikin jarida a Nijeriya, da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin kafafen yaɗa labarai da gwamnati, da al’ummar Nijeriya.