A yau ne wadanda suka yi rajistar kada kuri’a su 988,923 a kananan hukumomi 16 na Jihar Ekiti ke zaben gwamnan Jihar Ekitii.
Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da zaben ne a runfuna 2,445 na yankunan zabe 177 da ke mazabar majalisar dattawa 3 dana majalisar wakilai 6 a fadin jihar.
‘Yan takara 16 za su fafata a zaben gwamnan da za a yi, wanda zuwa ranar 13 ga watan Yuni al’umma sun karbi katin zabe 749,065 na wadanda suka yi rajista a jihar.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa za a tantace masu kada kuri’a ne tare da kada kuri’ar a lokaci daya.
Wadanda za su fafata a zaben sun hada da Abiodun Oyebanji na jami’yyar APC, Olabisi Kolapo na PDP, Olusegun Oni na SDP.
Sauran sun hada Reuben Famuyibo na Accord, Ajagunigbale Olajide na AAC, Oluwole Oluyede na ADC, Elebute-Halle Kemi na ADP da kuma Benjamin Obidoyin na jam’iyyar APGA.
Sauran da suke takarar kujerar gwamna sun kuma hada da Fagbemi Adegbenro na jam’iyyar APM, Christiana Olatawura na APP, Daramola Olugbenga Onile na LP, Fatomilola Oladosu na NNPP da Iyaniwura Ifedayo na jam’iyyar NRM.
Cikin wadanda za su fafata a zaben sun hada da Agboola Ben na jam’iyyar (PRP), Adebowale Oluranti Ajayi na YPP da kuma Adeolu Akinyemi na jam’iyyar ZLP.
Hukumar zabe ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za ta gudanar da sahihin zabe da zai samu karbuwa ga dukkan bangarorin