Ayau ranar Alhamis ce ake sa ran kotun koli zata raba gardama kan wanda yake da sahihancin tsaya takara a kujerar gwamna a karkashin Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa.
Umar Namadi ta bakin lauyansa, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya yi nasara a babbar kotun tarayya da ke Dutse da kuma kotun daukaka kara da ke Kano.
Amma, Aliyu, bisa daukaka karar da ya shigar mai lamba: SC/1453/2022 yana kalubalantar hukuncin da Kotun Daukaka Kara (reshen Kano) ta yanke a ranar 4 ga Nuwamba, 2022 wadda ta yi watsi da karar da ya shigar a baya tare da tabbatar da zaben Namadi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Jigawa. .
Kwamitin mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Ita Mbaba, a hukuncin da aka yanke ranar 4 ga watan Nuwamba, ya yi watsi da daukaka karar da Aliyu ya shigar a kan hukuncin ranar 13 ga Satumba, 2022 da mai shari’a Hassan Dikko na babbar kotun tarayya da ke Dutse, ya yi kan rashin bayar da hujjoji kwarara.