Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Jibrilla Bindow ya koma jam’iyyar PDP, inda ya jaddada goyon bayansa ga Gwamna Umaru Fintiri na sake tsayawa takarar gwamnan jihar.
Tsohon gwamnan wanda tsohon dan jam’iyyar APC ne, ya bayyana haka ga gwamna Fintiri ta hannun wata tawagar shugabannin kungiyoyin goyon bayansa 250.
- Ina Fatan Na Kammala Mulki Lafiya Na Koma Katsina – Buhari
- An Kubutar Da Mutum 6 Cikin Wadanda Aka Sace Yayin Harin Tashar Jirgin Kasa A Jihar Edo
Da yake jawabi a dakin taro na Banquet da ke gidan gwamnati a Yola a ranar Litinin, shugaban tawagar, Abdullahi Bakari, ya ce sun kai ziyarar ne bisa umarnin shugabansu.
A cewar jagoran, tsohon gwamnan, ya bukace su da su mika godiyarsa ga gwamna Fintiri na ganin an kammala ayyukan da ya gada a fadin jihar.
Sai dai sun ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya kasance jagoransu tsawon shekaru na bukatar goyon bayansu ga takararsa ta shugaban kasa.