Dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai san makomarsa dangane da karar da ya shigar kan kalubalantar ci gaba da tsare shi da jami’an tsaron farin kaya (DSS) ke yi.
Idan za a tuna a ranar 10 ga watan Yuni ne DSS ta kama gwamnan CBN jim kadan bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga aiki tare da bayar da umarnin a bincike a ofishinsa.
- ‘Yan Majalisar Dokokin Nijeriya Sun Bukaci Karin Albashi
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Umarci Masu Gidaje A Hanyoyin Ruwa Su Tashi
A karar da ya shigar ta hannun lauyansa, Joseph Daudu (SAN), a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, Emefiele yana zargin an tauye masa hakkinsa.
Wadanda aka shigar da karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya; Babban daraktan hukumar DSS, sai dai wadanda ake karar sun bukaci kotu ta yi watsi da karar duba da girman laifin da ake zarginsa da aikatawa.
A zaman da aka yi a ranar 20 ga watan Yuni, DSS, ta bakin lauyanta, I. Awo, ya shaidawa mai shari’a Hamza Muazu cewa tsare Emefiele ya dace, domin hukumar ta DSS ta samu umarnin wata kotun majistare da ke Abuja na ci gaba da tsare shi har sai an kammala bincike.
A nasa bangaren, lauyan Akanta-Janar na tarayya, Tijjani Ghazali (SAN), ya bayar da hujjar cewa kama Emefiele da tsare shi da hukumar DSS ta yi wani hukunci ne na bangaren zartarwa na gwamnati, don haka ya bukaci kotu da kada ta tsoma baki.
Sai dai lauyan Emefiele, Daudu, bai amince da su ba, inda ya jaddada cewa karar na kan hanya.
Mai shari’a Muazu ya dage zaman har zuwa yau domin yanke hukunci kan ko yana da hurumin sauraren karar da kuma duba bukatar Emefiele.