A wasu lokutan lashe kofi a matakin kasa yana daraja sama da na kungiya kuma kusan za a iya cewa kai tsaye lashe kofi a tawagar kasa yana bai wa dan wasa damar lashe kyautar Ballon d’Or.
Zakakuri kuma matashin ɗan wasan Spaniya da Barcelona, Lamine Yamal na dab da sauya tarihin kwallon kafar duniya nan da wasu ‘yan shekaru saboda yadda yake buga wasa cikin nasara.
Lamine Yamal, mai shekara 18 shi ne ya zo na biyu a takarar kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafar duniya ta Ballon d’Or kuma da a ce ya lashe kyautar a bikin da aka yi a birnin Paris a farkon makon nan, da ya zama dan wasa mafi kankantar shekaru da ya lashe gasar.
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere.
Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha.
Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru.
Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana cewa: yana da burin samun Ballon d’Or masu yawa idan ya samu dama.
Matasa da dama sun so Yamal ya lashe Ballon d’Or a wannan shekara, musamman irin kokarin da ya yi a bara, da kuma lashe kyautar gwarzon matashin danwasa da ya yi a bara. Kuma rashin samun kyautar ba ta yi wa matasa da dama dadi ba.
Ana ganin samun nasara a tawagar ‘yan wasan kasar Sifaniya zai fi ba shi damar lashe kyautar fiye da kungiyarsa ta Barcelona, amma idan har Barcelona ta iya lashe gasar cin kofin zakarun turai tabbas zai iya lashewa.
Amma kuma akan fifita nasarar da dan wasa ya yi a kasarsa fiye da kungiyar da yake bugawa wasa, kuma a bayyane take Kofin Duniya na daya daga cikin manyan abubuwan da zai sa mutum ya lashe kyautar.
Saboda haka idan har Sifaniya ta lashe kofin duniya a shekara mai zuwa ta 2026, Yamal zai iya samun kyautar Ballon d’Or. Kasancewar a yanzu yadda yake da cikakken gurbi a tawagar kasar, babu yadda za a yi Sifaniya ta ci kofin ba tare da kwallayensa ba.














