• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Mourinho Zai Koyar Da Kwallon Kafa A Kasashen Jamus Da Faransa?

by Abba Ibrahim Wada
1 month ago
Mourinho

A kwanakin baya ne kungiyar kwallon kafa ta Benfica ta nada shahararren mai koyarwa Jose Mourinho a matakin sabon kociyanta kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar wasa ta 2027.

Mourinho, mai shekara 62 ya maye gurbin Bruno Lage, wanda aka kora bayan da ya yi rashin nasara a gasar zakarun turai ta Champions League a gida a hannun kungiyar Karabag.

  • Matatar Dangote Ta Dawo Sayar Da Man Fetur A Kuɗin Naira
  • Firaministan Sin: Adalci Shi Ne Abu Mafi Daraja A Wurin Kasashen Duniya 

Tsohon kociyan na Chelsea da Manchester United ya sake komawa horar da kwallon kasa kasa da wata daya, bayan da ya raba gari da Fenerbahce, bayan da Benfica ta hana kungiyar ta Turkiya zuwa gasar zakarun Turai ta Champions League da aka fara.

Mourinho ya fara horar da kwallon kafa a Benfica a shekara ta 2000, amma wasanni 10 kacal ya ja ragama, sai ya bar kungiyar bayan rashin jituwa tsakaninsa da shugaban ƙungiyar na wancan lokaci.

A yarjejeniyar da suka kulla, Mourinho da kungiyar za su zauna don cimma matsaya ko zai ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa kakar gaba kwana 10 da zarar an kammala wasannin 2025/26.

LABARAI MASU NASABA

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama.

Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal. Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba.

Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup da

Portuguese Cup Chelsea (2004-07 da 2013-15) Premier League uku, FA Cup da League Cup uku. Inter Milan (2008-10) Serie A biyu, Champions League da Coppa Italia

Real Madrid (2010-13) La Liga, Copa del Rey, Manchester United (2016-18) Europa League da League Cup. Tottenham (2019-21) Bai ɗauki kofi ba. Roma (2021-24) Conference League. Fenerbahce (2024-25) Bai ɗauki kofi ba.

Mourinho ya yi suna a kungiyar FC Porto tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2004, bayan lashe kofi guda shida har da Champions League da ya dauka a kakar wasa ta 2003 zuwa 2004.

Tun bayan da ya bar kasarsa ta haihuwa a 2004, Mourinho ya horar da kungiyoyin Chelsea karo biyu da Inter Milan da Real Madrid da Manchester United da Tottenham Hotspur da Roma da kuma Fenerbahce. Bayan ya koma Benfica, Mourinho ya ce “babu daya daga cikin manyan kungiyoyin” da ya yi aiki tun da ya bar Benfica da ya ji a matsayin “girmama, alhaki ko kwazo”. Bayan da aka kori Lage ranar Talata, shugaban kungiyar, Rui Costa ya ce sabon kociyan da zai dauka sai mai tarihin lashe kofuna.

Hakan yana nufin Mourinho ne ya dace, bayan da ya lashe kofi 21 na baya-bayan nan shi ne Conference League a Roma a 2022, da kuma Champions League biyu da gasar rukuni-rukuni guda takwas a kasashe hudu, amma dai kofi na karshe da ya dauka shi ne Europa League.

Benfica za kuma ta je buga wasa a Newcastle United, sannan kuma za ta karbi bakuncin tsohuwar kungiyar da Mourinho ya horar Real Madrid a dai Champions League.

Benfica ta kare a mataki na biyu a teburin babbar gasar Portugal a bara, kuma rabonta da kofin tun 2022 zuwa 2023. Mourinho ya fuskanci takaddama a Turkiya, musammam yadda ya yi ta caccakar alkalan wasa na kasar, lamarin da ya kai ya samu rashin jituwa da su.

A watannin baya cikin watan Nuwamba, Mourinho ya zargi Fenerbahce da kin gaya masa gaskiya kan gogewar alkalan wasan kasar, amma ya ce Atilla Karaoglan shi ne wanda ya fi gwanninta lokacin da ya yi rafli da suka doke Trabzonspor.

Mourinho ya shigar da Galatasaray kara a watan Fabrairu, bayan da suka zarge shi da yin kalaman wariyar launin fata. Lokacin da aka nada Mourinho kociyan Fenerbahce a watan Yunin shekarar 2024, miliyoyin magoya baya sun yi kyakkyawan fata saboda suna ganin an dauki daya daga cikin fitattun masu horarwa a duniya wanda zai kawo karshen kamfar lashe kofi a shekaru da yawa da cewar kungiyar za ta taka rawar gani a gasar zakarun Turai.

Sai dai nan take mafarkin ya kasa zama gaske. Fiye da shekara daya, wannan mafarkin sai ya koma takaici. Mourinho ya kasa yin nasara a wasan hamayya na Istanbul derby kuma ya kasa daukar kofin babbar gasar kasar.

Yanzu dai ya koma kungiyar da ta fitar da Fenerbahce a wasannin cike gurbin shiga gasar Champions League ta bana. Wasu magoya bayan Fenerbahce na jin an yaudare su. Ba kawai Mourinho ya yadda su ba, ya kuma dauke su shashashai. Wasu suna ganin banda kungiyar kwallon kafa ta Benfica da Mourinho ya koma, kasar da ake ganin nan gaba zai iya komawa domin koyar da kwallon kafa ita ce kasar Saudiyya, idan har ya bar kungiyar Benfica, amma kuma har yanzu bai koyar da kungiya ba a kasar Faransa da Jamus. A shekarun baya an taba alakanta Mourinho da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen da Jamus kafin daga baya kungiyar ta dauki Pep Guardiola, sannan a Faransa ma shugabannin kungiyar Paris Saint German zun yi zawarcinsa a lokacin da kungiyar take neman mai koyarwar da zai jagorance ta zuwa lashe gasar cin kofin zakarun turai da suke nema ruwa a jallo.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
Wasanni

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya
Wasanni

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko
Wasanni

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
Next Post
Jami’an Tsaro Sun Ceto Fasinjoji 8 Da Aka Sace A Kogi

Jami’an Tsaro Sun Ceto Fasinjoji 8 Da Aka Sace A Kogi

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.