• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Ne Za A Ga Bayan Hare-haren Bindiga A Amurka?

by CMG Hausa
2 years ago
Bindiga

“Duk lokacin da na ga an sa hannu cikin jaka, na kan ji tsoro”, furuci ke nan na Osadolor Hernandez, wata daliba a jami’ar Chicago ta kasar Amurka, wadda ta ce, “Har ma ina tunanin ko zan haihu lokacin da na girma, sabo da ba na son ganin yara na suna fuskantar barazanar hare-haren bindiga da ka iya afka musu ba zata, abin da ke sa ni jin tsoro a rayuwata ta kowace rana.” Kalaman nata a hakika ya bayyana yanayin da Amurkawa da yawa ke ciki a halin yanzu.

A jiya ma an kai harin bindiga a wata cibiyar kasuwanci da ke bayan birnin Dallas na jihar Texas ta kasar Amurka, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, ciki har da yara. A wannan rana kuma, an ji harbin bindiga a unguwar Tacony ta birnin Philadelphia, lamarin da ya hallaka mutane biyu tare da jikkata wani.

  • Kasashen Sin Da Afghanistan Da Pakistan Sun Sha Alwashin Karfafa Hadin Gwiwar Inganta Tsaro

In an duba, kusan kowace rana irin wadannan hare-haren bindiga na faruwa a Amurka. A baya baya nan, a ranar 5 ga wata, wani dan bindiga ya harbe wata mace har lahira, tare da ji wa wani rauni a wani filin ajiye motoci da ke Annapolis na jihar Maryland ta kasar Amurka, kafin daga bisani dan bindigar ya kashe kansa.

Sai kuma a ranar 4 ga wata, wasu mutane 4 sun halaka sakamakon harin bindiga da ya faru a kauyen Moultrie da ke kudancin jihar Georgia. A ranar 3 ga wata kuma, an kai harin bindiga ga wani asibitin da ke birnin Atlanta, lamarin da ya halaka wata ma’aikaciyar lafiya, tare da jikkata wasu mutane 4……

Gwamnatin Amurka ta sha suka daga gida da ma waje sakamakon matsalar hare haren bindiga da ke ci wa kasar tuwo a kwarya.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Sakamakon matsin da gwamnati take fuskanta, a watan Yunin bara, Shugaban kasar Joe Biden ya sa hannu a kan wani shirin doka na kayyade bindigogi, sai dai abin takaici, yau kusan shekara guda ke nan, amma ko kadan ba a ga alamar kyautatuwar yanayin da ake ciki ba.

Alkaluman da shafin yanar gizo dake bayani game da matsalar harbin bindiga mai suna “Gun Violence Archive” ya fitar sun shaida cewa, a farkon watannin hudu na bana, mutane kusan dubu 14 sun mutu sakamakon hare-haren bindiga a Amurka, adadin da ya kai kimanin 115 a kowace rana ke nan. Sabo da rashin niyyar daidaita ainihin abubuwan da ke haifar da matsalar bindiga, ya sa shirin dokar ya kasa warware matsalar da ake fuskanta.

Tsohon shugaban kasar Amurka Franklin Roosevelt ya taba bayyana cewa, daya daga cikin ‘yancin dan Adam shi ne “’yanci na rashin jin tsoro”. To, amma kasar da ko rayukan jama’arta ta kasa karewa, ina ake zancenta game da ‘yanci da ma hakkin dan Adam?

Domin moriyar wasu gungun mutane, al’ummar Amurka na fama da munanan hasarorin rayuka. Ko yaushe ne za a ga bayan hare-haren bindiga a Amurka? (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Lardin Hunan Ya Samu Tagomashin Cinikayyar Waje Tsakanin Sa Da Kasashen Afirka A Rubu’in Farkon Bana

Lardin Hunan Ya Samu Tagomashin Cinikayyar Waje Tsakanin Sa Da Kasashen Afirka A Rubu’in Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.