• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Shugaban Kasa Zai Ba ‘Yan Matan Yobe Nasu Kyaututtukan

byMairo Muhammad Mudi
2 months ago
Yobe

A ‘yan makwannin da suka gabata, Nijeriya ta sake samun karuwa daga kwallon kafa zuwa kwallon Kwando, har ma da fagen ilimi a ketare; ‘yan matan Nijeriya sun yi nasara a duniya.

A kasar da galibi labarai marasa dadi suka fi yawa, wadannan nasarori uku sun zo ne a jere tare da tunatar da mu cewa; idan akwai dama da karfafa gwiwa, ‘yan matanmu za su iya samun kowace irin nasara a duniya.

  • CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Na “Sautin Zaman Lafiya” A Washington
  • Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu

Da farko dai, Super Falcons sun sake kafa tarihi ta hanyar lashe Kofin Mata na Afirka (WAFCON) na 2024 a Kasar Morocco. Bayan haka, D’Tigress, ‘yan kwallon kwando mata na Nijeriya, sun lashe Kofin AfroBasket na FIBA a karo na biyar a jere, lallai abin alfahari ne sosai.

Shugaban kasa ya nuna farin cikinsa ga wadannan nasarori ta hanyar ba su kyautar kudi har Dala100,000 ga kowace ‘yar wasa, gidaje da kuma kambun girmamawa ta kasa (OON). Babu shakka, wannan mataki ne da ya dace; sannan kuma abin a jinjina masa.

Sai kuma, wata nasara ta ban mamaki mai kuma matukar inganci, wanda ake zaton wuta a makera; kwatsam kuma sai ga ta a masaka.

LABARAI MASU NASABA

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

Me Ake Nufi Da Ado? 

‘Yan mata uku daga Jihar Yobe ta Arewa, Fatima Adamu, Falmata Bukar da Aisha Usman; sun wakilci Nijeriya a wata gasa ta Turanci da aka gudanar London, inda suka doke kasashe 69 da suka shiga gasar daga sassan fadin duniya. Ko shakka babu, wannan ba karamin abin alfahari ba ne a ce; daga yankin da galibi ake gani a matsayin guda cikin wadanda suka samu koma baya a fannin ilimi ga kuma talauci, amma wadannan ‘yan mata suka yi irin wannan bazata, ta hanyar lashe wannan gasa.

To sai dai, tambayar da ke ci wa mutane tuwo a kwarya ita ce; me yasa aka bi su da shiru da kuma ko in kula?

Me yasa aka yi wa Super Falcons da D’Tigress kyakkyawar kyauta, amma kuma aka bar ‘yan matan Yobe da sakon taya murna kawai daga fadar shugaban kasa? Ina kyautar girmamawa, ina kudi, ina gidaje, ina daukaka da su ma suka cancanta su samu?

Bari na fito a mutum, wannan ba kokari ne na rage kimar wadanda suka yi fice a fannin wasanni ba. Sun cancanci lambar yabo da suka samu, amma wannan yana kawo wasuwasi ga zukatan wasu, me yasa muke girmama shahara watanni fiye da hazaka a ilimi?

Tsawon shekaru, ana ba da muhimman kyaututtuka ga ‘yan wasa, mawaka da shahararrun mutane, yayin da masu hazaka a fannin ilimi da fasaha ke kasancewa a gefe.

Kamfanin MTN na Nijeriya, sun bayar da Naira miliyan 150 ga Super Falcons, amma har yanzu babu ko kwatankwacin haka ga ‘yan matan Yobe. Ina Kamfanin MTN, Glo, Dangote, BUA da sauran manyan kamfanoni?

Ko saboda daga Yobe suka fito ne, yankin da ya sha fama da rikice-rikicen Boko Haram da koma baya? Ko saboda nasarar ba ta dauki hankalin mutanen kudu a kafafen sada zumunta ba?

Abin da ya fi damun mutane shi ne, shugaban kasa ya san da nasarar, domin kuwa ya tura sakon taya su murna kadai. To, me ya hana a yi musu goma sha biyu ta arziki su ma? Wannan ya kara cusa shakku a zukatan jama’ar Arewa: Shin, shugaban kasa ya fi damuwa da ci gaban Kudu ne kadai ko kuwa?

Mutane da dama a Arewa, sun fara korafi game da yadda ake yi musu rikon sakainar-kashi bayan sun ba da goyon baya mai karfi a zaben shugaban kasa fiye da yankin da ya damu da su a yanzu. Haka zalika, abin takaicin shi ne; yadda manya-manyan jigajigan gwamnati daga Arewa suka yi shiru, watakila saboda kariyar kujerunsu, amma wannan shirun ka iya haifar da rashin yarda ga shugaban kasa, saboda haka; ya kamata su gane cewa, ba taimakon sa suke yi ba.

A wannan gaba, dole ne mu yaba wa Gwamnan Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, wanda bai jira fadar shugaban kasa ba, ya karbi ‘yan matan; wanda tun farko shi ne ya dauki nauyinsu, ya kuma girmama su, ya nuna yana alfahari da su, ya kuma yi alkawarin tallafa musu. Wannan shi ne irin shugabancin da ake bukata.

Amma ya kamata a fahimci cewa, wannan nasara ba ta Jihar Yobe ba ce ita kadai, nasara ce ta Nijeriya baki-daya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da damar gyara wannan kuskure ta hanyar bai wa wadannan ‘yan mata irin girmamawar da suka cancanta a ba su. Wannan zai isar da sako mai karfi ga iyayen Arewa:

’Ya’yanku mata, suna da hazakar da Nijeriya ke alfahari da ita. Wannan zai sa yara yin tururuwa zuwa makaranta.

Haka kuma, zai dawo da martabar ilimi a kasa da yawan samun daukaka a fannin wasanni da shahara fiye da basira da ilimi.

Saboda haka, shugaban kasa, har yanzu muna jiran mataki mai kyau a kan wadannan ‘yan mata na Yobe.

Fatima, Falmata da Aisha, sun yi wa Nijeriya hidimar da za a yi alfahari da su. Yanzu kuma, lokaci ne da Nijeriya ita ma za ta sa su yi alfahari da ita.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano
Bakon Marubuci

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

October 3, 2025
Me Ake Nufi Da Ado? 
Bakon Marubuci

Me Ake Nufi Da Ado? 

September 26, 2025
Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka
Bakon Marubuci

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 30, 2025
Next Post
Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA

Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version