Al’ummar Jihar Kaduna na ci gaba da zaman zulumi; bisa karuwar rashin tsaro, lamarin da ya tilasta wa wasu barin garuruwansu ba tare da sun shirya ba.
Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa, karshen ‘yan ta’adda ne ya zo, musamman ganin yadda jami’an tsaron Nijeriya suka datse hanyoyin da ke da hadaka da junansu a dazukan da suke zama da kuma karancin makamai da suke fama da shi yanzu.
- Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya
- Majasirdin Sarkin Zazzau, Alhaji Yusuf Saleh Barde Ya Rasu
Hasali ma sun bayyana cewa, yawaitar garkuwa da mutane a Jihar Kaduna, wata alamace da ke nuna cewa kwanakin ‘yan ta’addan sun zo karshe a jihar kamar yadda suka shaida wa LEADERSHIP Hausa.
Har ila yau kuma, wasu na ganin Gwamnatin Jihar Kaduna; karkashin jagorancin Sanata Uba Sani, na da matukar sassaucin ra’ayi wajen yaki da wadannan ‘yan ta’adda, sabanin gwamnatin da ta shude ta Malam Nasiru El-Rufa’i; wacce ta rika yin fito-na-fito da masu tayar da kayar-baya a jihar.
Wakilinmu, ya yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Lamuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwa, domin jin irin matakan da suke dauka wajen samar da tsaro a fadin jihar, amma abin ya ci tura. Duk da haka, wakilinmu bai yi kasa a guiwa ba; domin kuwa ya tura masa sakon tes, bai ba da amsa ba, haka nan kuma ya kai ziyara ofishinsa; nan ma bai samu damar ganawa da shi ba.
A wata ganawa da hukumomin tsaro a jihar ta Kaduna kwanan na, Gwamna Uba Sani ya yi kira da a kaddamar da tsarin tsaro na bai-daya, ta hanyar inganta cudanya da jama’a gami da wayar da kan al’ummar; kan muhimmacin samar da tsaro.
Bugu da kari, Gwamna Uba Sani ya sha alwashin samar da dukkanin kayan aikin da suka dace ga hukumomin na tsaro, domin samun damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a fadin jihar ta Kaduna baki-daya.
A zantawarsa da wakilinmu, Dakta Yahuza Getso; masanin tsaro a Nijeriya da kasashen Afirka ya bayyana cewa, matsalar rashin tsaro a Jihar Kaduna; abubuwa ne guda hudu: “Abu na farko shi ne, dole ne sai jami’an tsaro sun tashi tsaye wajen tabbatar da dakatar da wadannan hare-hare da ake kaiwa, duk kuwa da cewa; jami’an tsaron suna yi bakin kokarinsu wajen kai hari ga ‘yan ta’addan, wanda hakan ya sanya su kuma ‘yan ta’addan suka tunzura tare da kai hare-hare a kan al’ummar da ba su ji ba, ba su kuma gani ba.
“Abu na biyu shi ne, akwai abin da masu iya magana ke cewa, ‘Tusa ta kusa kure wa Bodari’, dalili kuwa, yanzu haka karfin wadannan ‘yan ta’adda ya yi matukar raguwa, sakamakon hana shiga da kayan masarufi na rayuwa da kuma takura musu da aka yi wajen ci gaba da samun makaman da suke yin ta’addanci da su, saboda idan ka dubi irin yadda suke kawo hare-hare a halin yanzu, ba sa zuwa da makamai duk da cewa suna diban mutane da dama.
“Abu na uku kuma shi ne, jami’an tsaro sun datse hanyoyin da suke samun hadaka da junansu, inda suke kai komo a cikin dazukan, saboda haka; sai suke ganin babu wata mafita sai dai su rika daukar mutane masu yawa, wanda hakan zai jawo hankalin hukumomi ko da za a kai musu hari; za a koma tunanin cewa akwai wasu mutane masu a tare da su masu yawan gaske, don haka wajibi ne a daga kafa wajen kai musu farmaki.
“Kazalika, abu na hudu shi ne; idan aka ci gaba da samun bayanai daga al’umma, babu shakka jami’an tsaron sojojin wannan kasa, za su kakkabe kafatanin wAdannan ‘yan ta’adda.
“Batun da suke yi yanzu na neman kudin fansa, wanda kowa ya sani cewa ya wuce hankali, abu ne wanda suke yi domin kara razana al’umma da kuma jefa musu zaman zuLlumi, amma su shugabannin jami’an tsaron Nijeriya, suna kara samun kaimi ne idan suka ji ‘yan ta’addan na neman irin wadannan makudan mudade, wanda hakan ke nuna cewa; lallai karfinsu ya fara karewa; suna neman kudin sayen makamai da sauran makamantansu”.
“Saboda haka, mafita kadai yanzu ita ce; shugabanni su kara jin tsoron Allah, sannan kuma su tuna irin nauyin da Allah ya dora musu, wanda zai tambaye su wata rana. Haka nan, su ma jami’an tsaron; su kara kaimi tare da sanin cewa, wannan yaki da suke yi da ‘yan ta’adda; wata rana ko shakka babu za a kai ga cimma gaci. Saboda haka, ka da su samu sanyin guiwa a kan irin fadi tashin da ake yi, sannan kuma dole ne a kara dankon zumunta tre da fahimtar juna a tsakanin jami’an tsaro da sauran al’umma, wanda hakan zai taimaka wajen samun bayanan sirri da kuma sa ido, domin kara taimakawa wajen samun nasarar yakin da ake yi wajen kawar da wadannan ‘yan ta’adda a fadin yankin baki-daya”, in ji Dakta Getso.
A nashi bangaren, Malam Muhammad Garba, Tsohon Malamin Makaranta ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna, sannan kuma mai yin fashin baki a kan harkokin siyasar ta Jihar Kaduna ya bayyan cewa, akwai hasashen da ake yi cewa, Gwamnatin Uba Sani; na da sassauci a kan harkokin tsaro, lamarin da ake ganin shi ne silar samun yawaitar matsalar rashin tsaron a fadin jihar.
“Lokacin Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i; ya hana kowa sakat, domin kuwa ya yi amfani da wasu bangarori na jami’an tsaro tare da sa ido a kowane lungu da sako, ya kuma kokarin tarwatsa wadannan ‘yan ta’adda; har sai da ta kai ga babu wani mai iya yin motsi a jihar.
Wannan dalili ne, ya sa aka samu saukin yawaitar ire-iren wadannan hare-hare na ‘yan ta’adda a fadin jihar, amma yanzu ana ganin wannan gwamnatin ta Uba Sani, tana da matukar sassauci;” in ji shi.
Jibrin Aliyu Kuriga (Dan Bala), mazaunin garin Kuriga ne da ke cikin Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna, ya bayyana cewa, shi ne mutum na farko da ‘yan bindigar suka fara yin garkuwa da shi a tarihin wannan gari, inda ya kwashe kimanin kwanaki 53 a hannunsu; kafin da aka biya kudin fansa ya shaki iskar ‘yanci, a cewar tasa; “Wallahi cikin kwanaki 53 da na kwashe a hannunsu, ban taba sa ruwa na wanke fuskata da shi ba; haka nan duk hannayena sun sha duka, wanda ban taba tunanin za su ci gaba da aiki a gaba ba”.
“Mu tara aka kwashe, amma bayan an yi sulhu da ‘yan bindigar daga baya sai suka sako mutum biyar; sauran hudun kuma suka kashe su. Saboda haka, mu al’ummar Jihar Kaduna; musamman mu da muke yin rayuwa a wajen jihar, shakka babu rayuwarmu na cikin wani mayuwacin hali na zaman zulumi, bisa wannan matsalar ta rashin tsaro da muke fama da ita,” a ta bakinsa.
Wani mai sana’ar sayar da Gawayi a Jihar Kaduna, Malam Abdulkarim Jibrin, ya bayyana cewa, ko shakka babu rashin tsaro ya shafi sana’ar kasuwancinsu, musamman su da suke shiga kauyuka suna gudanar da kasuwancinsu, wanda a halin yanzu ‘yan ta’adda duk sun ta da wadannan kauyuka baki-daya.
“Duk inda za ka je ka sayo itace da gawayi, yanzu babu sakamakon tashin kauyakan da ‘yan ta’addar suka yi, sannan kuma ai duk garin da a yau aka ce babu kauye, ya zama nakasasshe komai girmansa. Mu dai yanzu, wanzuwar ‘yan bindiga ya taba rayuwarmu da ta iyalinmu “.