Nijeriya ta shaida lalacewar babbar tashar wutar lantarki daga tushen ba da wuta sau shida kenan a cikin 2024 zuwa ranar Litinin, a yayin da layin lantarkin ya lalace daga megawatts 2,583.77 da karfe 2 na dare, inda ya ci gaba da aiki bayan an masa gyare-gyare.
Ko da yake kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya ta misalta wannan lalacewar baya-bayan nan da faruwar ibtila’in gobara, sai dai ta jima tana daura laifin matsalar rashin samun wadataccen wuta ga karancin samun iskar gas da kuma lalata turaku da layukan wutar lantarki a Nijeriya wanda suke ke janyo lalacewar wutar.
- Bangaren Amurka Ya Mayar Wa Bangaren Sin Da Kayayyakin Tarihi 38 Da Suka Bata Daga Sin
- Sharhi: Kokarin Fahimtar Yanayin Tattalin Arzikin Sin Ta Bangarorin Ayyuka Guda 3
Nijeriya na samar da matsakaicin wutar lantarki mai girman 4,000MW ga a kalla mutum miliyan 200 a fadin kasar.
Sai dai kash, wannan lamarin bai samuwa yadda ake tsammani ba sakamakon yawan lalacewar wutar lantarki da katsewarsa da ake dangantawa da karancin samun gas, lalata kayan aikin lantarki da matsalolin kudi hadi da sauransu.
Lokacin da wutar ta lalace a ranar Litinin, harkokin kasuwanci da hada-hadar jama’a a sassa daban-daban na Nijeriya ya samu koma-baya, inda jama’a suka yi ta korafi, musamman a yankin kudu maso gabas.
Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun tabbatar da cewa sun samu rashin samun wutar ne daga tushen samar da wutar lantarki, inda suka bai wa kwastomominsu hakuri da cewa da zarar suka samu wadataccen wuta daga tushen da suke samun wutar za su sake ga kwastomominsu.
Wasu ‘yan Nijeriya da aka zanta da su, sun nuna damuwarsu, inda suka nemi a shawo kan matsalar yawaitar lalacewar wutar lantarki a kasar nan.
Sai dai hukumar TCN ta ce bayan lalacewar wutar a ranar Litinin a wannan ranar aka samu nasarar gyarawa domin wuta ta dawo, ta misalta lalacewar wutar da cewa an samu tashin gobara ne a cibiyar raba wutar lantarki ta Afam.
A wata sanarwa da mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ya fitar a Abuja, ya ce gobarar ta janyo tsaiko na rashin wuta na dan kankanin lokaci a fadin kasar nan.