Al’ummar duniya yanzu sun kai biliyan takwas, bisa hasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta yi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya ce hasashen na zuwa ne don murna da samun zaman lafiya da ci gaban da aka samu duk da bambance-bambance da ake dashi, sannan kuma muyi dubi da alhakin da aka daura wa bil’adama na kula da duniyarsa.
Majalisar Dinkin Duniya ta danganta wannan ci gaban, da samun ci gaban dan Adam, yayin da yake rayuwa mai tsawo sakamakon inganta lafiyarsa, samun abinci mai gina jiki, tsaftarsa da kuma cigaba a fannin samar da magunguna.
“Haka zalika sakamakon karuwar yawan haihuwa, musamman a kasashe masu fama da karancin arziki na duniya – wadanda akasarinsu suna yankin kudu da hamadar Sahara – lallai yawan haihuwa na ci gaba da jefa yankin cikin hadari,” in ji Guterres.
Da take magana kan hasashen cewa Mutanen duniya sun yi yawa, shugabar asusun kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya (UNPF), Natalia Kanem, ta ce, “Wasu na nuna damuwa cewa, duniyarmu ta cika da yawan jama’a. Ina tabbatar muku cewa, yawan al’umma ba barazana ce ba ga cigaban al’umma sai da kara samun cigaban al’ummar.”
Yawan jama’a a yanzu ya ninka sau uku fiye da kididdigar da aka yi a duniya biliyan 2.5 a shekarar 1950.