A jiya ne, aka gudanar da taron kolin raya fasahar sadarwar zamani na kasar Sin karo na 5 a birnin Fuzhou dake lardin Fujian. A yayin bikin bude taron, hukumar kula da bayanan yanar gizo ta kasar Sin ta fitar da rahoton ci gaban kasar Sin a wannan fanni a shekara 2021.
A cewar alkaluman kididdigar raya fasahar sadarwar zamani ta kasar Sin ta shekarar 2021, daga shekarar 2017 zuwa 2021, yawan bayanan da kasar Sin ta fitar, sun karu daga zettabytes 2.3 zuwa zettabytes 6.6, kuma zettabyte 1 na bayanan, ya yi daidai da tiriliyan 500 na hoton da mutum ke dauka da kansa, da wakokin MP3 guda tiriliyan 2.5.
Bayanan da ake samarwa, ya kai kashi 9.9 cikin 100 a fadin duniya a cikin shekarar 2021, wanda ke matsayi na biyu a duniya baki daya. Kasar Sin ta gina ababen more rayuwar jama’a ta fannin fasahar sadarwa mafi girma da kuma ci gaban fasaha a duniya.
Ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta gina tashoshi na fasahar 5G miliyan 1.425, wanda ya kai sama da kashi 60 cikin 100 na adadin da ake da su a fadin duniya, kana masu amfani da fasahar 5G miliyan 355, da kashi 100 cikin 100 na kauyuka da kauyuka masu fama da talauci, suna iya yin amfani da yanar gizo.
A halin yanzu, yadda masana’antu na kasar Sin ke amfani da Intanet, ya shafi fannoni 45 na tattalin arzikin kasa, haka kuma hada-hadar cinikayya ta intanet ta karu daga yuan tiriliyan 29 a shekarar 2017 zuwa yuan tiriliyan 42 a shekarar 2021.(Ibrahim)