Mataimakin babban sakataren bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitarwa daga kasar Sin na Canton, kuma mataimakin darektan cibiyar cinikayyar waje ta kasar Sin, Wen Zhongliang, ya bayyana yayin taron dandalin tattaunawa kan sabbin damammaki na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka da yammacin Asiya jiya Lahadi cewa, bikin baje kolin na Canton wata muhimmiyar kafa ce ga kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, kuma muhimmin dandali ne na kasuwancin kasashen waje na kasar.
Tun da aka kafa shi shekaru 67 da suka gabata, bikin baje kolin ya tara kudaden fitar da kayayyaki zuwa ketare da suka kai kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.5, da kuma masu sayayya kusan miliyan 10 daga ketare wadanda suka halarci bikin baje kolin ta yanar gizo da kuma a zahiri, haka kuma bikin ya taka muhimmiyar rawa, wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashe daban daban ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)