Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 1.37, wanda ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na watan Agusta. Yawan kudin shiga da na kashewa da ya shafi kudaden kasashen waje na kasar Sin a farkon rabu’i na uku na bana ya kai dalar Amurka triliyan 11.6, wanda ya kai matsayin koli a tarihi, kana ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.
Mataimakin shugaban hukumar kuma kakakin hukumar Li Bin ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye samun karuwar cinikin waje, yawan kudin shiga a fannin cinikin kaya ya ci gaba da samun karuwa, kana an kiyaye samun hada-hadar kudi a fannonin samar da hidimomi da zuba jari a tsakanin kasa da kasa.
Li Bin ya bayyana cewa, tun daga farkon bana, an tafiyar da kasuwar kudaden waje ta kasar Sin yadda ya kamata yayin da ake fuskantar yanayi na rashin tabbas a kasashen waje, kuma an kiyaye kyakkyawan zaton yadda kasuwa za ta kasance, da tabbatar da yanayin hada-hadar kudaden waje, inda hakan ya shaida karfin kasar Sin a wannan fanni. (Zainab Zhang)