Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ta fitar da kididdiga a yau Alhamis, wadda ta nuna yadda daga watan Janairu zuwa Agusta na bana, yawan jarin da Sin ta zuba a ketare, a bangaren da ba na hada hadar kudade ba, ya kai kimanin dalar biliyan 80, adadin da ya karu da kashi 18.8%, in an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Daga cikin adadin, yawan kudaden da kamfanonin Sin suka zuba a kasashen da shawarar “ziri daya da hanya daya” ta shafa, kai tsaya a bangaren da ba na hada hadar kudi ba, ya kai kimanin dalar biliyan 19.2, wanda ya karu da kashi 22.5% bisa na makamancin lokaci na bara.
Hukumar ta kuma nuna cewa, tun farkon shekarar bana, hukumar ta gabatar da ayyuka daban daban, na janyo jarin waje, mai taken “shekarar zuba jari ta kasar Sin”. Kuma masu zuba jari na ketare sun dora babban muhimmanci kan hakan, da ma nuna kwarin gwiwa wajen shiga ayyukan.
Kaza lika, hukumar ta ba da labarin cewa, Sin da Turai sun yanke shawara bayan tattaunawa, cewa za su gudanar da tattaunawar manyan jami’ai a fannin tattalin arziki da ciniki karo na 10 a ranar 25 ga wannan wata a nan birnin Beijing. (Amina Xu)