Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, tun daga farkon shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, tsarin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya jure wa matsin lamba, inda cinikin kayayyaki ya kai matsayi na farko a duniya.
An bayyana haka ne a yau Juma’a, yayin taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala ingantaccen shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14”, wanda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar.
Ma’aikatar ta kara da cewa, kason kayayyaki da hidimomi da ake shige da ficensu tsakanin Sin da kasashen waje ya ci gaba da samun tagomashi inda suka kai fiye da kaso 10 da kaso 14 bisa dari. Sikelin cinikin ba da hidimomi kuma ya kai matsayi na biyu a duniya. Kana ingancin jarin waje ya karu, inda yawan jarin waje da Sin ta samu tun daga farkon shirin shekaru biyar-biyar na 14 ya zarce dalar Amurka biliyan 700 da aka yi hasashen zai kai.
Har ila yau, Sin ta ci gaba da jan hankalin jari daga kasashen waje, har ana ci gaba da kyautata tsarin zuba jarin. Hadin gwiwar kasa da kasa a fannin samar da kayayyaki kuwa na samun ci gaba cikin tsari. Matsakaicin karuwar jarin da Sin ta zuba a kasashen waje ya kai fiye da kashi 5 bisa dari a kowace shekara, wanda ke matsayi na daya daga cikin manyan kasashe uku na duniya, kuma ayyukan gine-ginen da Sin ta yi a kasashen waje gaba daya sun karu cikin kwanciyar hankali. Bugu da kari, Sin ta sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa ta samar da kayayyaki da dama tare da kasashen dake gina shawarar Ziri Daya da Hanya Daya tare. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp