Wasu takardun sanarwa sun nuna cewa, a shekarar 2023 da ta gabata, yawan jarin waje na kai tsaye da Sin ta zuba ya kai dala biliyan 177.29. Adadin da ya karu da kaso 8.7 bisa dari kan na makamancin lokaci na shekarar da ta gabaci hakan. Kana adadin ya kai kaso 11.4 bisa dari cikin jimillar ta duniya baki daya. Cikin adadin, wanda Sin ta zuba a kasashen Afirka ya kai dala biliyan 3.96, adadin da ya ninka sau 2.2 kan na makamancin lokaci na shekarar 2022.
A Talatar nan ne ma’aikatar cinikayya ta Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar dake lura da hada hadar musayar kudade ta kasar suka fitar da bayanan, bisa taken “Bayanan kididdiga na yawan jarin waje na kai tsaye da Sin ta zuba a shekarar 2023 “.
Bayanan sun kuma nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar ta 2023, masu zuba jari na Sin sun kafa kamfanoni har 48,000 a kasashe da yankunan waje 189, wadanda ke kunshe da ma’aikata kusan miliyan 4.3, wadanda suka kunshi kaso 60 bisa dari na ma’aikata ‘yan kasashen waje. (Mai fassara: Saminu Alhassan)