• English
  • Business News
Sunday, July 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yawan Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Takwas Na Bana A Sin Ya Karu Da Kaso 5.4%

by CGTN Hausa and Sulaiman
9 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Yawan Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Takwas Na Bana A Sin Ya Karu Da Kaso 5.4%
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman gudanar da ayyukan jigilar kayayyaki daga watan Janairu zuwa Agusta na bana a yau Asabar. Bayanan sun nuna cewa, yawan jigilar kayayyaki a zamantakewar Sinawa ya karu da kashi 5.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.

Dangane da yawan jigilar kayayyakin masana’antu a watan na Agusta kuwa, samfuran fasaha kamar mutum-mutumin inji na masana’antu, da hadadden alluna laturori ko IC, sun ci gaba da habaka cikin sauri, kuma saurin bunkasar su ya kai kusan kashi 20 cikin dari.

  • Kasar Sin Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaba A Duniya
  • Zulum Ya Gabatar Da Ƙarin Kasafin Kuɗi Naira Biliyan 61 Ga Majalisar Borno

Dangane da yadda ake cin gajiyar hakan, yawan jigilar kayayyakin kamfanoni, da na al’ummar kasar a farkon watanni takwas na bana ya karu da kashi 7.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. A cikin wannan adadi kuma, bukatar jigilar kayayyakin ta yanar gizo ta fi saurin habaka, fiye da ta jigilar kayayyakin sayarwa na zahiri.

Labarai Masu Nasaba

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

Dangane da fannin shige da fice kuwa, daga watan Janairu zuwa Agusta, jimillar yawan jigilar kayayyakin da ke shigowa ta karu da kashi 4.3 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, yayin da jimillar yawan jigilar kayayyakin da ake fitarwa ta karu da kashi 5 cikin dari, bisa na makamancin lokacin bara.

Dangane da masana’antu, a watan Agusta, jimillar yawan jigilar kayayyakin masana’antar kera na’urorin lantarki, da na sadarwa, ta karu da kashi 11.4 cikin dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara, wanda hakan ya taimaka wajen habaka bunkasuwa a bangarorin masana’antu, da kasuwanci, da sauran fannoni. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yadda Rayuwa Take A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Nijeriya

Next Post

Gobarar Motar Makaranta Ta Hallaka Fiye Da Yara 20 A Thailand

Related

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali
Daga Birnin Sin

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

12 hours ago
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal
Daga Birnin Sin

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

13 hours ago
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

14 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
Daga Birnin Sin

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

15 hours ago
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu
Daga Birnin Sin

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

17 hours ago
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

18 hours ago
Next Post
Gobarar Motar Makaranta Ta Hallaka Fiye Da Yara 20 A Thailand

Gobarar Motar Makaranta Ta Hallaka Fiye Da Yara 20 A Thailand

LABARAI MASU NASABA

Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos

Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos

July 6, 2025
Kofin Duniya: Real Madrid Za Ta Fara Da PSG A Semi Final

Kofin Duniya: Real Madrid Za Ta Fara Da PSG A Semi Final

July 6, 2025
Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund

Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund

July 6, 2025
Tsoro, Fargaba Da Wahala: ‘Bala’in Da Muka Gani A Yakin Sudan

Tsoro, Fargaba Da Wahala: ‘Bala’in Da Muka Gani A Yakin Sudan

July 6, 2025
Bayern Munich Ta Fara Zawarcin Marcus Rashford

Bayern Munich Ta Fara Zawarcin Marcus Rashford

July 6, 2025
Gobe Za A Fara Wasannin Kofin Afirka Na Mata

Gobe Za A Fara Wasannin Kofin Afirka Na Mata

July 6, 2025
Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

July 5, 2025
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

July 5, 2025
‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

July 5, 2025
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.