Masu aiko da rahotanni na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, watau CMG, a yau sun gano daga wani taron tsara aiki na ma’aikatar sufuri ta kasar Sin cewa, ana sa ran adadin kai-komon mutane a tsakanin lardunan kasar Sin zai kai kimanin biliyan 64.5 a shekarar 2024, lamarin da ke nuna an samu karin kaso 5.2 cikin dari a mizanin shekara-shekara.
Bugu da kari, duk dai a banar, kasar Sin tana sa ran kammala jigilar kayayyakin kasuwanci da ta kai kimanin tan biliyan 56.5, da ke nuna an samu karin kaso 3.5 cikin dari a mizanin shekara. Kana ana sa ran kasar ta kammala jigilar kayayyaki ta teku kimanin tan biliyan 17.5, wadda ta karu da kaso 3.4 a mizanin shekara, inda hakan ke nuna hada-hadar kasuwancin cikin gida da ta kasashen waje za su karu da kaso 1.9 da kuma kaso 7 cikin dari bi-da-bi a mizanin shekara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)