Yau Alhamis, mataimakin ministan kasuwanci kana mataimakin wakilin Sin a shawarwarin kasa da kasa Ling Ji, ya yi bayani kan yanayin habakar bude kofar Sin ga ketare.
Ling Ji ya bayyana a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya cewa, ya zuwa karshen bara, yawan kamfanonin da aka kafa da jarin waje ya zarce miliyan 1.23, kana yawan kudin waje da aka yi amfani da shi ya zarce dalar Amurka triliyan 2.8.
A kwanakin baya, majalisar gudanawa ta Sin ta zartas da shirin ba da tabbacin shigo da karin jarin waje na shekarar 2025, abin da ya aike da sako mai yakini na habaka bude kofar Sin ga ketare. Kuma ya bayyana niyyar gwamnatin Sin ta daukar karin manufofin dake karawa jarin waje kwarin gwiwar shigowa kasar.
Bugu da kari, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sha nanata cewa, buga karin harajin kwastam da Amurka ta yi ya sabawa ka’idojin WTO. (Amina Xu)