Bisa alkaluman da kamfanin layin dogo na Sin wato China Railway ya fitar, a rubu’i na uku na bana, jigilar kayayyaki ta jiragen kasa ta kara inganci, kuma yawan kayayyakin da jiragen kasa na Sin suka yi dako a rubu’i na uku na bana, ya kai ton biliyan 1.004, adadin da ya karu da kaso 3.8 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. A sa’i daya kuma, hakan ya kafa sabon tarihi na jimilar kayayyakin da aka yi dako a rubu’i daya tak, wanda ya shaida cewa an samu gagarumin ci gaba, a fannin gina tsarin jigilar kayayyaki ta layin dogo na zamani.
Za a iya ganin cewa, da farko, karfin jigilar kayayyaki ya karu. Layukan dogo na Sin sun rika amfani da matsakaitan jiragen kasa dubu 182 a kowace rana, adadin da ya karu da kaso 4.1 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.
- Yadda Muka Dakatar Da Yunkurin Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC – Kungiyar Arewa Ta Tsakiya
- Beijing Na Shirin Fadada Yankin Gwaji Na Motocin Hawa Masu Tuka Kansu
Na biyu kuma, an yi amfani da jiragen kasa masu saurin tafiya cikin inganci. A rubu’i na uku na bana, layukan dogo na Sin sun yi jigilar da manyan kwantenoni har miliyan 9.58, adadin da ya karu da kaso 17.3 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.
Na uku, karfin ba da hidimomin jigilar kayayyaki ya kara inganci. Hukumomin da abin ya shafa sun inganta fasahohin zamani na jigilar kayayyaki, wanda ya sa aka kai ga gudanar da harkokin jigilar kayayyaki ta yanar gizo gaba daya, ta yadda aka kara samar da sauki ga abokan ciniki.
Na hudu, gyare-gyaren tsarin aiwatarwa da suka shafi kasuwanci na jigilar kayayyaki sun ci gaba da karfafa. Hukumomin da abin ya shafa sun habaka gyare-gyaren da suka shafi kasuwanci, mai nasaba da farashin jigilar kayayyaki ta layin dogo, da aiwatar da dabarun daidaita farashi bisa fannoni, da yanayi, da nau’i da kuma karfin sufuri, kuma sun ci gaba da samar da riba ga kamfanoni na taimakawa zamantakewa. (Safiyah Ma)