Ma’aikatar kasuwancin Sin ta gabatar da yanayin cinikin kayayyakin masarufi na Sin a rubu’in farko na bana yau Alhamis.
A cewar ma’aikatar, a rubu’i na farko, yawan kudaden da al’ummun kasar Sin suka kashe kan kayayyakin masarufi na yau da kullum ya kai yuan triliyan 12.5, wanda ya karu da kashi 4.6 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.
- Xi Ya Gana Da Sarkin Cambodia Da Manyan Jami’an Kasar
- Sin Da Malaysia Za Su Samar Sabbin Shekaru 50 Masu Muhimmanci Na Dangantakar Kasashen Biyu
Ban da haka, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar, He Yongqian, ta bayyana cewa, ma’aikatar ta ci gaba da tattaunawa a fagen aiki tare da hukumomin da abin ya shafa na bangaren Amurka. Inda ta ce, matsayin bangaren Sin a bayyane yake, wato yana maraba da tattaunawa tare da bangaren Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya.
He Yongqian ta kara da cewa, bangaren Sin na fatan kokari tare da bangaren Turai, don kiyaye tsarin cinikayya bisa ra’ayin bangarori daban daban tare da kungiyar WTO a matsayin tushensa da bin ka’idojin cinikayya.
Game da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137, wanda aka fi sani da Canton Fair dake gudana, He Yongqian ta ce, ya zuwa yanzu, masu sayayya fiye da dubu 110 daga kasashe da yankuna 216 sun halarci bikin, adadin ya karu da kashi 10 cikin dari bisa na karo na 135. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp