An bude taron koli na raya kasar Sin a bangaren yanar gizo, karo na 6 a yau Alhamis a birnin Fuzhou. Yayin bikin bude taron, ofishin sadarwa da yanar gizo na kasar Sin, ya gabatar da rahoton bunkasuwar yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2022.
Rahoton ya nuna cewa, a bara, yawan mutane da suka yi amfani da yanar gizo ya kai fiye da biliyan 1, adadin da ya kai kashi 75.6% kan na yawan al’ummarta. Kaza lika yawan kudaden dake shafar tattalin arzikin yanar gizo na kasar ya kai fiye da triliyan 50, wanda ya kai matsayi na biyu a duniya.
Ban da wannan kuma, rahoton ya ce, ya zuwa karshen shekarar bara, Sin ta bude tasoshi masu samar da hidimar yanar gizo ta 5G fiye da miliyan 2.3, kuma yawan mutanen dake amfani da fasahar ta 5G ya kai fiye da miliyan 561, wanda ya kai kashi 60%, bisa jimillar na duniya baki daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp