Rahotanni daga taron shugabannin hukumomin kula da harkokin ikon mallakar ilimi na kasar Sin sun ruwaito cewa, harkokin ikon mallakar ilimi na kasar sun samu ci gaba sosai a shekara ta 2024, inda yawan lambobin mallakar kere-kere na kasar ya kai miliyan 4.756.
Kazalika, yawan lambobin mallakar kere-kere na duniya na PCT, da yawan tamburan da aka nemi izinin mallaka bisa yarjejeniyar Madrid, gami da yawan fasalin hajojin da aka nemi izinin mallaka bisa tsarin Hague, duk suna kan gaba a duniya. Har wa yau kuma, adadin lambobin mallakar kere-keren da suka shafi sabbin sana’o’i bisa manyan tsare-tsare, ya kai miliyan 1.349, adadin da ya karu da kaso 15.7 bisa dari. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp