Yayin da aka kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 9 ko CIIE a birnin Shanghai na kasar Sin, masharhanta na ci gaba da fashin baki kan tasirin baje kolin na bana, tare da bayyana gamsuwa game da kyawawan sakamako da aka cimma cikin kwanaki 6 na gudanarsa.
Manyan alkaluma 5 da ake la’akari da su yayin bikin na CIIE na bana, sun kafa sabon tarihi, inda baje kolin ya samu adadin kamfanoni mahalarta har 4,142, kuma a karon farko, girman filin baje kolin ya kai murabba’in mita 444,000, kana girman sassan da kamfanoni suka baje hajojinsu ya kai murabba’in mita 370,000.
Haka kuma, sama da kamfanoni 300 daga cikin manyan kamfanoni mafiya karfi a duniya sun halarci baje kolin na bana. A daya bangaren kuma, adadin kayayyakin da aka gabatar a karon farko a mataki na kasa da kasa, da wadanda aka gabatar a matakin nahiyar Asiya, da a matakin kasar Sin ya kai 485. Ana kuma hasashen yawan harkokin cinikayya da aka yi niyyar aiwatarwa cikin shekara guda, wadanda aka daddale yarjejeniyarsu yayin baje kolin, sun kai darajar kudi har dalar Amurka biliyan 85.45, wanda hakan ke nuni da karuwar kaso 2.3 bisa dari idan aka kwatanta da bikin CIIE na bara.
A bana, baje kolin CIIE ya hallara baki daga kasashe da yankunan duniya 162, baya ga hukumomin kasa da kasa. Ga tarin masu baje hajoji na kasashen ketare, baje kolin ya wuce batun halartar dandalin cinikayya na kwanaki shida. Domin kuwa sun samu zarafin kulla alakokin kasuwanci masu dorewa, da kuma damar ci gaba da shiga katafariyar kasuwar kasar Sin mai kunshe da tarin sabbin damarmaki, da kofofin shiga sabbin sassan hadin gwiwar cinikayya.
A wannan gaba da ake samun karuwar matakan buga haraji daga wasu sassa, da tarnakin kasuwanci dake illata tsarin gudanar da hada-hadar cinikayya, duniya na da matukar bukatar gudanar da budadden tsarin kasuwanci sama da kowane lokaci a baya. Don haka, muna iya cewa baje kolin CIIE na bana, ya aike da wani muhimmin sako mai shaida aniyar kasar Sin ta kin amincewa da kariyar cinikayya, da wanzar da bude kofofinta na kasuwa ga dukkanin duniya baki daya, ta yadda sassan kasa da kasa za su ci gaba da more damarmaki tare, ba tare da wata wariya ba.Ga ’yan kasuwar kasashen waje, baje kolin CIIE ya samar musu da damar haduwa da Sinawa masu yin odar hajoji daga ketare, da masu rarraba su, da masu sayar da su a cikin kasar, har ma da masu amfani da su duk a wuri guda.
Ga wasu kamfanonin kuwa, baje kolin dama ce ta gabatar da sabbin kayayyakinsu, da lalubo damarmakin da babbar kasuwar Sin ka iya bayarwa.
A daya bangaren kuma, ga kasashe masu tasowa, damar shiga babbar kasuwa mafari ne kawai. Masu fitar da hajoji daga irin wadannan kasashe na da bukatar nemo masu saye, da fahimtar abubuwan da masu sayayya suka fi bukata, da tantance sharuddan kasuwa, da ma tantance kalubale da ake iya fuskanta domin magance matsalolin cinikayya.
Kuma dukkanin wadannan sun samu a yayin baje kolin na bana.Muna iya cewa wannan baje koli na CIIE, wata dama ce mai muhimmanci ta haduwar masu saye da masu sayarwa na bangarorin duniya daban daban, wanda ba ya ga zarafin kulla huldodi, zai kuma samar da karin damarmaki na fahimtar juna tsakanin ’yan kasuwar sassa daban daban na duniya. Kana tuni ya zama babban dandalin dake zaburar da damar ’yan kasuwa daga kasashe masu tasowa, ta fadada hada-hada musamman ta kayayyakin amfanin gona, da fadada samar da guraben ayyukan yi ga manoma da inganta sarrafa hajoji da sauransu.
Ko shakka babu baje kolin CIIE ya zamo kakkarfar dama ga dukkanin al’ummun duniya ta cin gajiyar hada-hadar kasuwanci ba tare da barin ko wane bangare a baya ba. Kuma hakan ya kara fayyace himmar kasar Sin a fannin raya damarmakin tana ci gaba tare da dukkanin sassan duniya, ta yadda za a kai ga “Gudu Tare A Tsira Tare!













