Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ba da rahoto a yau Talata, cewa daga watan Janairu zuwa Yuli na bana, yawan ribar da masana’antu masu matsakaicin kudin shiga suka samu ya kai dalar biliyan 575, wanda ya karu da kashi 3.6% bisa na makamancin lokaci na bara.
Daga cikinsu, masana’antu masu dogaro da kimiyyar zamani suna sahun gaba, inda a tsawon wannan lokaci, yawan ribar da suka samu ta karu da kashi 12.8% bisa na makamacin lokacin bara.
Ban da wannan kuma, yawan ribar masana’antun samar da na’urori ya karu da kashi 6.1% bisa na makamancin lokaci na bara, wanda hakan ya nuna dorewar karuwarsa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp