Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a yau Juma’a cewa, yawan shinkafar da kasar Sin ta samu a farkon kakar bana, ya karu da kashi 0.4 bisa dari a bana, matakin dake nuna yadda manufofin tallafin gwamnati suka haifar da sakamako mai gamsarwa.
A cewar hukumar NBS, shinkafar da aka noma ta kai tan miliyan 28.12, karuwar tan 106,000 daga matakin shekarar 2021. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp