Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka.
An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata ya zarce dala miliyan 7, inda fim din ya zama mafi shahara a matakin koli da Sin ta gabatar a karshen makon a Amurka.
An ce, an fara nuna wannan fim a gidajen sinima 770 dake arewacin Amurka daga ranar 14 ga watan nan da muke ciki, a matsayin fim din da Sin ta gabatar, kana yawan kudin da ake samu wajen nuna fim din da kuma yawan kallonsa a sinima duk sun kai matsayin koli cikin shekaru 20 da suka gabata a wannan yanki.
Bayan haka, kafofin yada labarai a bangaren fina-finai sun lura da cewa, “Ne Zha 2” zai zama fim na farko da ba na Hollywood ba, wanda yawan kudin da zai samu zai shiga sahun gaba a cikin fina-finai 20 mafi karbuwa a tarihin film na duniya, sun kuma yi kiyasin ci gaban karuwar kudin har ya zarce na fim din “Inside Out 2”, kana zai zama matsayin koli a bangaren fina-finan “Cartoon”, kuma daya daga cikin fina-finai 10 mafi samun kudin shiga a tarihin fina-finan duniya. (Amina Xu)