Kididdigar da hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi ta yi nuni da cewa, zuwa karshen watan Maris din shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ya kai kilowatt biliyan 3.43, adadin da ya karu da kaso 14.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Daga cikin wutar lantarkin da ake samarwa, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa bisa makamashin hasken rana ya kai kilowatt miliyan 950, adadin da ya karu da kaso 43.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kazalika, a sa’i daya kuma, yawan wutar lantarki da kasar ke iya samarwa bisa karfin iska ya kai kilowatt miliyan 540, adadin da shi ma ya karu da kaso 17.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp