A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki.
Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa kaimi wajen ingiza yakin cinikayya, ‘yan siyasa da wakilan manyan kamfanonin Amurka na haye wahalhalu inda suke ta kawo ziyara Sin, wanda hakan ke nuni ga matukar goyon baya da salon bude kofar cinikayyar duniya ke samu, da kuma fatan da ake yi na samun cikakken daidaito, da hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
Ko shakka babu, matakin Amurka na kaddamar da yakin cinikayya ta fakewa da “kishin farfado da tattalin arzikin kasa”, ba zai sauya halin da ake ciki na gibin kasuwancin Amurka ba, ko ingiza farfadowar sashen sarrafa hajoji na kasar. Maimakon haka, matakin zai haifar da yanayi ne na koma bayan tattalin arziki, tare da jefa rayukan Amurkawa cikin mummunan yanayi, wanda kuma zai kai ga mayar da Amurka saniyar ware tsakanin kasashen duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp