Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce mafi yawan ‘yan siyasar Nijeriya ba su da tarbiyya tun daga ƙuruciyarsu, shi ya sa suke aikata cin hanci da rashawa.
Sanusi ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a daren ranar Laraba.
- Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bayar Da Kiwon Lafiya Kyauta Ga ‘Yan Fansho Masu Karamin Karfi
Ya ce mutane da dama da ke riƙe da muƙamai a gwamnati, ba a koya musu gaskiya da riƙon amana ba tun suna yara.
“Yawancinsu sun shiga gwamnati ne saboda dalilai marasa kyau. Ba su da tarbiyyar shugabanci,” in ji shi.
Sanusi ya ce: “An rusa ɗabi’u da tarbiyyar kirki a ƙasar nan. Mutanen da ke mulki yanzu ba su da tarbiyya kuma ba su da wani abu na ƙwarai da za su bari a baya.”
“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.”
Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu.
“Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi.