Za a gudanar da taron kolin BRICS karo na 16 a birnin Kazan na kasar Rasha daga yau Talata zuwa Alhamis na wannan mako, shugaban kasar Sin Xi Jinping na halartar taron. Kasancewar taron farko da aka gudanar bayan BRICS ta shigo da karin kasashe 5 a bara, kuma shi ne sabon babi na hadin gwiwa tsakanin mambobin. Shugabannin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 za su tattauna kan batun hadin kan kasa da kasa.
Tsarin BRICS da ma ya kasance wani dandali inda aka nemi daidaito tsakanin mambobinta, yanzu ya zama wata alama ga sabuwar makomar bil Adama, wanda ke wakiltar fatan da ake da shi na raya tattalin arzikin duniya bisa adalci. Sin wani muhimmin jigo ne dake ingiza hadin kan mabambantan bangarori. Ban da wannan kuma, tsarin ya samar da wani muhimmin dandali ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa, da kuma dandalin samun bunkasuwa tare da cin moriya tare. Lamarin dake bayyana ma’anarsa a wannan sabon zamani. Ruhinsa mai nacewa ga bude kofa da yin hakuri da juna da ma samun moriya tare ya zama tubalin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda ya samu karbuwa matuka. A wani bangare na daban, tsarin ya dace da bukatun kasashe masu tasowa na samun bunkasuwa tare.
A matsayin daya daga cikin kasashe wadanda suka kafa tsarin, Sin ta dade tana nacewa ga shi, inda ta ba da gudummawa sosai wajen jagorantar wannan tsari. Ba shakka, tabbas taron a wannan karo zai taka rawar gani wajen samar da tabbaci da ma’ana mai yakini ga duniya dake fuskantar sauye-sauye bisa kokarin mambobi kasashen BRICS, da yadda za a ci gaba da kara azama ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Hadin gwiwar da ake yi bisa wannan tsari na da makoma mai haske. (Amina Xu)