An gudanar da karamin dandalin tattauna kan ci gaba mai dorewa na kasashe masu tasowa da hadin gwiwar Sin da Afirka, dake karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar tattalin arzikin duniya na Hongqiao karo na 7 jiya Talata, inda mahalarta suka tattauna kalubalolin da kasashe masu tasowa suke fuskanta a kokarinsu na inganta samun ci gaba mai dorewa, a sa’i daya kuma sun tattauna yadda aka cimma damammaki na ajandar samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030 ta MDD ta hanyoyin inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa da sauransu.
A cewar ministan cinikayya da masana’antu na kasar Rwanda, Prudence Sebahizi, matsalar zuba jari da karancin makamashi da kuma karancin abinci, su ne manyan kalubaloli guda uku da kasashe masu tasowa suke fuskanta. Ministan ya kara da cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, da sauran shawarwarin dake shafar duk duniya guda uku da Sin ta fitar, sun samar da dimbin alfanu ga kasashe masu tasowa da suka hada da Rwanda.
Bugu da kari, ministan kasuwanci da cinikayya da masana’antu na Zambia, Chipoka Mulenga, ya bayyana cewa, kasashen Afirka suna fuskantar kalubaloli daban daban yayin da suke neman samun ci gaba mai dorewa, kamar karancin fasahohin zamani. Ya ce a halin yanzu, fasahohi suna bunkasa cikin sauri, amma akwai wahala kasashen Afirka su tafi da zamani. Don haka, ana bukatar kasashe dake da buri daya da Afirka kamar Sin su tallafawa nahiyar, domin samun ci gaba tare.(Safiyah Ma)