Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa ‘ya’ya mata miliyan 7.6 ne a Nijeriya, musamman wadanda akasarinsu suka fi yawa a arewacin kasar ne, aka tauyewa damar samun ilimin Boko.
Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Cristiana Munduate ta sanar da hakan a jihar Kano a yayin bikin zagayowar ranar ‘ya’ya mata ta duniya ta shekarar 2023.
- Jirgin Sojoji Ya Yi Wa ‘Yan Ta’adda Luguden Wuta A Zamfara
- Gwamnatin Bauchi Ta Kori Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wikki Tourist
Taron wanda ya gudana a dakin taro na gidan gwamnatin Kano takensa shi ne: “Yanzu ne lokacinmu da sanin ‘yancinmu domin gobenmu ta yi kyau.”
Kazalika ta bayyana cewa, a Nijeriya ana da adadin kashi 15 a cikin dari, na yaran da suka daina zuwa makarantar Boko.
Bugu da kari, kashi 9 a cikin dari kacal ne, na ‘ya’ya mata wadanda iyayensu talakawa ne suka zuwa makarantun sakandare.
Ta yi nuni da cewa, sai dai duk da wannan kalubalen akwai fatan da muke da shi.
A cewarta, a yanzu jihar Kano ita ce ta biyu na yawan ‘ya’ya matan da suka daina zuwa makarantar Boko a fadin kasar nan.
Har ila yau, wasu daga cikin daliban da suka halarci bikin ranar sun yi magana akan lamura da dama, ciki har da kalubalen rashin tsaro wanda suka bayyana a matsayin babban ginshikin da ya zama tarnaki a neman ilimin na ‘ya’ya mata wanda hakan ya dakile su daga gina gobensu.