- Hauhawar Farashi Ya Kai Kashi 35
- Za A Samu Sauki A Nan Gaba – Gwamnati
Yayin da ake gaba da shiga bikin Kirsimati babban lamarin daya damu ‘yan Nijeriya shi ne yadda za su iya da kansu a wannan shekara ta 2024, yawancin ‘yan Nijeriya suna jira ne suka yadda za ta zo masu, domin tuni sun saba da kasancewa cikin kunci na rayuwa domin farashin kayayyaki kara tashin gwauron zabo yake yi.Tabarbarewar tattalin arziki yana ci gaba da damuwar magidanta saboda abinda yake shigo masu ta zai iya taimaka masu ba wajen tafiyar da rayuwarsu.Tabarbarewar rayuwa ta sa milyoyin ‘yan Nijeriya ba za sui ya yin bikin Kirsimati ba wanda suka saba da yi duk shekara.Kayan abinci lamarin zurga- zurga, kai har ma wasu kayan masarufi yanzu abin ya zama wata rijiya da ake kira da suna ‘mai da ka sha’ hakan yasa magidanta kansu ya daure domin lokacin da za ‘a shiga na farinciki ne amma hakan ba zata samu ba sai dai kawai ayi ta yin yake.
Yayin da tsadar farashin kaya ya karu da kashi 33.88, a watan Oktoba daga kashi,32.70 a watan Satumba 2024, farashin wasu nau’in kayayyaki musamman ma kayan gona kamar Shinkafa, mangyada, tumatari, da sauransu, sun karu da fiye da kashi 100 a shekara daya data gabata.
- Gwamna Lawal Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 546 Na Shekarar 2025
- Yadda Minista Ya Kaddamar Da Ginin Radio House Da Aka Yi Wa Kwaskwarima A Abuja
Alal misali, buhun shinkafa,wanda ake saidawa Naira 107,000 ne, wanda a shekarar 2023 ana sayar da shi Naira30,000 .Farashin lita 5 na mangyada da ake sayarwa Naira 6,000 a shekarar data gabata yanzu ana sayar da shi Naira 19,000.Hakanan ma farashin gas na girki ya ninka a cikin shekara daya a wasu wurare, hakan ta sa wasu iyalai suna fuskantar babbar matsala su samu damar yin abincin da suka saba yi lokacin irinbikin Kirsimati dake tafe.Sai dai duk da yake an yi karin mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya da wasu Jihohoi suka yi, kudaden da suke shigo ma jama’a abin ba a cewa komai, saboda matsin tattalin arziki, abinda wasu masana tattalin arziki ke cewa abin ya munana kwarai.
Idan aka yi la’akari da tsadar rayuwa da kuma yadda kudade basu shigowa ‘yan Nijeriya kamar yadda aka saba shekarun baya, kamar yadda Bankin duniya ya kiyasta yawan mutanen da suke zama cikin fatara ya karu da milyan 87.5 a shekarar 2023 zuwa milyan 104 a 2024, hakan na nuna an samu karuwar mutane milyan 17.
Ga mutane masu dama kowace rana matsin tattalin arziki ya sa mutane suna sauya tsarin tafiya hutu da suka yi. Bernard Kenechi, wani mai fashi kan a;’amuran yau da kullum, ya ce zai zaune Legas shi da iyalansa maimakon su je Kirsimati garinsu Aba saboda matsin tattalin arziki. “Babban burin shi kamar yadda yace shi ne ya tabbatar da yara sun kasance cikin farinciki,inda ya jaddada ya dace a ba da muhimmanci ga bukatun iyali ba maganar kudaden da za’a kashe zuwa hutu ba.
‘Yan kasuwa suna lamarin bai kyale su ba suna ji a jikinsu. A kasuwanni kamar Wuse a Abuja da Balogun a Legas, masu sayar da kayan abinci sun ce babu ciniki mutane nasu zuwa da yawa. Mrs. Funmilayo Amodu, mai sayar da abinci a kasuwar Iyana Iba a Legas ta nuna rashin jin dadinta, “Abubuwa da rayuwar duk sun yi tsada da yawa ga shi kuma babu kudade a hannun jama’a. Idan akwai kudi mutane za su zo su saya wurin mu, amma yanzu jira kawai muke sai lokacin da suka zo.”
A shekarun baya, kasuwanni za su cika da mutane masu saye suna neman abubuwan da za su saya bayan sun taya farashin, amma a shekarar 2024, lamarain yana da ban tsoro.Halin matsin tattalin arziki yasa ‘yan Nijeriya da dama basu da niyyar zuwa wani hutu, yanayin ya bar ‘yan Nijeriya da tunanin ina za su sa kansu idan lokacin ya yi.
Abn ba a iya cewa komai karuwa take yi lamarin kuncin rayuwa domin akwai ‘yan Nijeriya da dama wadanda su matsalarsu basu san yadda za su yi bai dan lokacin hutun ya yi.Masana sun bada shawarar cewa idan ba mataki aka dauka ba, matsalar za ta kara kwabewa ba tare da an samu wani ci gaba ba, kan tsarin tattalin arziki wadanda suke cikin fatara, lamarin nasu yana iya kara jagulewa yayin da suke rayuwa ta hannu baka – hannu kwarya. Kwararre kan tafarkin ci gaba tattalin arziki a Jami’ar Adeleke, Farfesa Tayo Bello, yace ‘yan Nijeriya na cikin wani mawuyacin halin kuncin rayuwa saboda tabarbarewar tattalin arziki.
Ga yawancin ‘yan Nijeriya, karuwar farashin rayuwa ta sa sun yi zabin da basu. “Samuel Okonkwa wani ma’aikaci a Abuja yace wannan shekarar ba za su je gida Kirsimati ba,”. “ Akwai dai maganar kudin makarantar yara da kuma kudin haya wadanda sun fi kyau a far gamawa da su kafin ayi maganar wasu bukukuwa can daban. Ko maganar sayen Kaza saboda shagalin Kirsimati yanzu ta zama wata abar da sai an yi tunani tunani tukuna.”
Jaridar NATIONAL ECONOMY ta lura da cewar a wasu kasuwanni mutane sun zauna ne kawai, suna Kallon masu saye suna fita ba tare da tayawa ba bare ma su saya ba,. “Ina nan tun da safe, na sayar da ‘yan kofunan shinkafa ne” cewar Chinyere Okonkwo, wata ‘yar kasuwa da take sayar da kayan abinci fiye da shekara goma. “Shekarar data gabata mutane sun sayi buhunan shinkafa da katon- katon na mai. Wannan shekaru kuwa suna tambayar farashin ne daganan su yi tafiyarsu.Komai dai ya yi tsada’’.
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 34.6.
Bayanai na baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 34.6 cikin 100 a watan Nuwamba daga kashi 33.8 a watan Oktoba.
A cikin rahotonta na Nuwamba da aka buga a ranar Litinin game da farashin kayan masarufi, Hukumar NBS ta ce, adadin ya nuna karuwar kashi 0.72 cikin 100 idan aka kwatanta da na Oktobar 2024.
“A kowace shekara, farashin kayan na farawa da kashi 6.40 sama da adadin da aka rubuta a watan Nuwamba 2023 (28.20%),” in ji ofishin.
“Wannan ya nuna cewa hauhawar farashin kaya (shekara-shekara) ya karu a watan Nuwamba 2024 idan aka kwatanta da wannan watan a shekarar da ta gabata (watau Nuwamba 2023).
“Bugu da kari kuma, a duk wata-wata, hauhawar farashin a watan Nuwamba 2024 ya kai kashi 2.638, wanda ya kai kashi 0.002 kasa da adadin da aka samu a watan Oktoba 2024 na kashi (2.640).
“Wannan yana nufin cewa a cikin Nuwamba 2024, kimar daraja a matsakaicin matakin farashi ya dan ragu kadan fiye da adadin karuwar matsakaicin matakin farashi a cikin Oktoban 2024.”
Ofishin ya kuma lura cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Nuwamba 2024, ya kai kashi 39.93 bisa100 a duk shekara, kashi bakwai cikin 100 sama da kashi 32.84 cikin 100 da aka samu a watan Nuwamban 2023.
Habakar farashin kayan abinci a kowace shekara ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki kamar haka; Dawa, Water Yam, Coco Doya, da dai sauransu ( Dankali, Dawa da Sauran nau’insu), Masara ta Guinea, Shinkafa, da sauransu (Ajin Burodi da Cere-als), Beer, Pinto (Ajin Taba), da Man dabino, Kayan lambu Man fetur da dai sauransu, da kuma abin ya shafi (Ajin mai da mai),” in ji NBS.
Sai dai kuma, a duk wata, ofishin ya ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Nuwamban shekarar 2024 ya kai kashi 2.98 cikin 100, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 0.05 cikin 100 idan aka kwatanta da na kashi 2.94 da aka samu a watan Oktoban 2024.
Sauran Jihohi kamar Delta ya karu da (kashi 26.47), Benue (kashi 28.98), da Katsina (kashi 29.57).
Hukumar NBS ta bayyana cewa Yobe ya karu da (kashi 5.14), Kebbi (kashi 5.10), yayin da Anambra (kashi 4.88) sun fuskanci hauhawar farashin abinci a wata, yayin da Adamawa ya karu da (kashi 0.95), Osun kashi (1.12), Kogi kuma (kashi 1.29) sun sami karuwar farashin a hankali.
“An danganta tashin gwauron zabin da aka samu a matsakaicin farashin kifin Mudfish, Busashen Kifi, Busasshen Kifi Sadine, da dai sauransu, wannan (Ajin Kifi) kenan. Sai Shinkafa, Garin Dawa, Hatsin Gero, Garin Masara, da sauransu (Ajin Bread da Cereals), Kwai, Madara mai karfi, Fresh Milk, da sauransu (Madara, cukui da ajin kwai, (Ajin Nama) busasshen naman sa, Naman Akuya, daskararrun kaji, da sauransu.,” in ji Ofishin.
“Matsakaicin hauhawar farashin abinci na shekara-shekara na watanni goma sha biyu da suka gabata, Nuwamba 2024 a kan watanni goma sha biyu da suka gabata ya kasance kashi 38.67, wanda ya zama kashi 11.58 sama da matsakaicin da aka samu a canjin shekara-shekara da aka samu a watan Nuwamba 2023 kashi (27.09).”