- Buhari Ya Matsa Kaimin Nada Magajinsa
- Sabon Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai A Jam’iyyar
- HalinDa Sauran Jam’iyyu Ke Ciki Kan Takarar Shugaban Kasa
A yayin da jam’iyyar PDP ta kammala babban taronta inda ta gudanar da zaben fid da gwani na wandan zai tsaya mata takarar shugabancin kasa a zaben da za a gudanar a shekarar 2023 a makon da ya gabata, a halin yanzu kallo ya koma farfajiyar jam’iyya mai mulki ta APC wanda ta dage gudanar da nata taron zuwa ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni 2022 bayan da hukumar zabe INEC ta kara wa’adin mika sunayen ‘yan takara.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya samu nasarar zama babban kwamandan takarar PDP bayan da ya samu kuri’a 371 a cikin kuri’u 767 da aka tantance aka kada, inda mabi da shi, Gwamnan Jihar Ribas ya samu kuri’a 237, Tsohon shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya zo na uku da kuri’a 70 sai tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim wanda ya tashi da kuri’a 14, kana Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed kuma ya samu kuri’a 20, shi kuwa Udom Emmanuel ya tashi ne da kuri’a 38.
Dele Momodu, Ayo Fayose, Charles Ugwu, da kuma Chikwendu Kalu duk sun tashi a tutar babu ma’ana basu samu komai ba.
Masu tsokaci a kan al’amurran siyasar kasar nan sun jinjina wa yadda jam’iyyar PDP ta gudanar da taron tare da nasarar da ta samu a na fitar da dan takara ba tare da gagarumar baraka ba, duk da wani na ganin cewar jam’iyyar ba ta cika alkawarin da ta yi wa ‘yan kudancin Nijeriya ba na mika takara zuwa yankinsu, wasu na ganin kusoshin jam’iyyar sun yaudari ‘yan kudu ne, musamman ganin yadda Gwamnan Jihar Sakkwato Waziri Tambuwal ya janye daga takarar ya kuma umarci magoya bayansa su kada kuri’arsu ga Atiku Abubaka a daidai lokacin da ake gab da fara kada kuri’a. Masana na ganin wannan takun ne ya taimaka wajen samun nasarar da Atiku don in ba ta haka ba da Gwamnan Ribas, Wike ne zai kai labari.
A jawabinsa na nasarar da ya samu, Abubakar Atiku ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin da ake fuskanta na tsaro a fadin kasar nan tare da tabbatar da hadin kan kasa in an zabe a matsayin shugaban Nijeriya a shekarar 2023, ya kuma nemi ‘yan jam’iyyar da ‘yan Nijeiya gaba daya su kawar da son rai su rungumi juna tare da aiki tare don don samun nasarar PDP a zaben 2023 da ke tafe.
A jawabinsa tun da farko, shugaban kwamitin shirya taron, Sanata Dabid Mark, ya nuna bakin cikinsa a kan yadda jam’iyyar APC ta lalata al’amura a Nijeyiya, ta kawo tashin hankali da kashe-kashen al’umma a sassan kasa, ya ce a halin yanzu ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka, suna gallalaza wa mutane, gwamanati ta kasa yin wani abu. Ya ce, wadannan su ne manyan dalilan da jam’iyyar ke neman sake dawowa kan karagar mulki don ta ceto kasar daga tabarbarewa.
Wannan nasarar da PDP ta samu na zabar Atiku ya tayar da hankalin jam’iyyar APC musamman ganin cewa, dattawa da shugabannin yankin arewa karkashin jagoracin Janar Aliyu Gusau da tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Bababangida na da daga cikn wadanda suka nemi ‘yan takarar da suka fito daga Arewa su janye su bar wa Atiku don suna ganin shi ne yake da cikakken karfin da zai iya karawa tare da samun nasara ga PDP. Wanda hakan ke nuna kamar Atiku ya samu karbuwa a Arewa kenan. Bayani ya nuna cewa, sai da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da kansa ya kira Tanbuwal ya nemi ya janye kuma ya amsa ba ma kawai ya janye ba har ma ya tabbatar da shi da magoya bayansa za su zabi Atiku.
A halin yanzu dai an fara shirye shiryen fito da wanda zai yi wa Atiku mataimaki, cikin wadanda ake sa ran za a iya zaba sun hada da Gwamna Wike wanda ya zo na biyu a zaben fidda da gwani, in har kuma bai karba ba to ana iya zaba a cikin Gwamnan Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi da kuma Gwamnan Abiya. Ana ganin dattawan na Arewa da suke goyon bayan Atiku za su jagoranci ganin an zakulo wanda zai samu karbuwa a sassan kasar nan.
APC Ta Sake Dabarun Fuskantar Zaben 2023
Tun kafin jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taronta suke ta kulli-kucciya da APC, kowacce jam’iyya na son sanin irin tsare-tsaren da abokiyar adawarta ke yi don ita kuma ta san irin matakin da za ta dauka don ta samu galaba a kanta. Nasarar da Atiku Abubakar ya samu na zama dan takarar jam’iyyyar PDP ta matukar girgiza APC inda nan take suka fara shirye-shire gudanar da nasu babban taron kamar yadda suka tsara, a ranar Litinin kawai kwamitin tantance masu takarar neman tsaya wa APC shugabancin kasa ya tantance mutum 12.
Daya daga cikin na gaba-gaba cikin masu takarar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bayan tantance shi da aka yi, ya bayyana cewa, shi ba zai janye wa kowa ba, ya ce, bai yarda da tsarin fitar da dan takara ta hanyar maslaha ba, ya kuma bayyana karara ga kwamitin tantancewar karkashin shugabancin tsohon shugaban jam’iyyar John Oyegun a zaman da suke yi a Otal din Trascorp Abuja. Cikin wadanda aka tantance zuwa lokacin hada wannan rahoto akwai tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Ameach, Abubakar Badaru; Tsohon karamin ministan Ilimi Emeka Nwajuiba, Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun; da kuma wanda ya yi Shugaba Buhari mataimaki a zaben 2011, Fastor Tunde Bakare, da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Saura sun hada da Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabe Umahi; tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima; Sanata Ajayi Boroffice; da mace tilo a cikin masu takarar, Barr (Misis) Uju Kennedy Ohnenye, da kuma Fasto Nicholas Felid Nwagbo, Mutum 25 ne dai suka yankin tikitin neman takarar shugabancin kasar nan a APC.
Buhari Ya Yi Taron Gaggawa Da Gwamnonin APC
Ganin yadda al’amurra suka tafiya ba kamar yadda aka zata ba, musamman yabon da ake wa PDP kan gudanar da babban taronta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira taron gaggawa inda ya gana da gwamnoni 22 da shugaban jam’iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu. A yayin taron, Shugaba Buhari ya fito karara yana rokon gwamnonin da su goya masa baya ya zabi wanda zai gaje shi da zai samu karbuwa wajen ‘yan Nijeriya gaba daya.
A sanarwar da babban jami’in watsa labarun shugaban kasa, Mista Femi Adesina ya sanya wa hannu, Shugaba Buhari ya bayyana wa gwamnonin cewa “Harkokin zaben 2023 sun kankama a halin yanzu na kuma lura da cewa, duk wata jam’iyyar da za ta yi ikirarin samun nasara sakamaon cikkaken hadin kai ne na ‘yan jam’iyyar dole kuma jam’iyyar mu ta APC ta yi koyi da haka.
“Adaidai lokacin da nake shekarar karshe ta wa’adin mulkina a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawar Nijeriya da kuma jagorar jam’iyyarmu, na fahimci cewa, jam’iyyar na matukar bukatar na bayar da jagorancin da zai kai mu ga nasarar kamar yadda muka tsara.
“Wannan jagorancin na da matukar muhimmanci a wannan lokacin, ta haka za mu kara fadada tare da kara jihohin da muke da su a yanzu.
“A ‘yan kwanakin nan za mu yi babban taronmu inda za mu zabi wanda zai daga mana tuta a zaben 2023, wanda za mu zaba yana da muhimmanci don dorewar akidun jam’iyyarmu.”
Shugaban kasa ya nemi gwamnonin su tsayu wajen taimaka masa a fitar da wanda zai iya fuskantar halin da ake ciki a yanzu, tare da la’akari da bukatar al’ummar Nijeriya da na duniya baki daya, ya ce, za a cigaba da tattauanawa da masu ruwa da tsaki don tabbatar da an tafi da kowa da kowa.
Gwamnan Jihar Kebbi, kuma shugaban kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC, Atiku Bagudu ya mayar da jawabi kan hakan, inda ya yi alkawarin bayar da dukkan goyon baya ga Shugaba Buhari don samun nasarar zabo wanda zai iya gadar Shugaba Buhari wajen kishin kasa da aiki tukuru.
“Za mu hada kai da shugaban kasa don samun nasarar gudanar da babban taron jam’iyyarmu,” in ji shi. Bayan taron da suka yi da shugaban kasa, gwamnonin sun shiga taron sirri inda aka yi hasashen za su tattauna wanann sabon barakar da matsayar shugaba Buhari za ta iya haifarwa,.
Tabbas zabin da PDP ta yi wa Atiku ya sanya APC tunanin bullo da wasu dabaru don tunkarar zaben 2023, kamar yadda jigo a APC kuma tsohon gwamnan Abiya, Sanata Orji Kalu ya bayyana a hirarsa da manema labarai bayan sanar da Atiku a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, a halin yanzu tunda PDP ta zabi dan takara daga arewa, to dole APC iya ma ta fito da dan takararta daga Arewan in har tana son ci gaba da mulki a 2023.
Ya kara da cewa, ya kamata APC ta zabo wani daga arewa maso gabas tun da Atiku daga yankin yake.
“Daga abin da ya faru a PDP a halin yazu ba zai kyautu mu zabi dan takara daga Kudu ba sai dai in muna son yi wa kanmu ritaya ne a siyasance,” in ji shi.
A kan haka ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya tilasta wa APC fito da wani daga arewa maso gabas. ‘Yan APC da dama sun yi na’am da wannan ra’ayi na Kalu, musamman wadanda suka fahimci irin tasirin da Atiku Abubakar zai iya yi a kakar siyasar Nijeriya ta 2023.
Sabon Rikici Ya Barke A APC
Wani kalubale da ke fuskantar APC kuma a halin yanzu, shi ne wani sabon rikici da ya kunno kai a jam’iyyar. Wannan rikici ne tsakanin shugabannin jam’iyyar inda mataimakan shugaban jam’iyyar 2 suka yi kira ga sauran shugabanin jam’iyyar su yi wa Abdullahi Adamu tawaye sabo yadda yake yanke shawarar gudanar da harkokin jam’iyyar ba tare da tuntubar kwamitin zartaswar jam’iyyar ba.
A sanarwar da suka sanya wa hannu ranar Talata, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa ta yamma, Salihu Mohammed Lukman, da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Kudu maso yamma, Isaac Kekemeke, sun gargadi shugaban jam’yyar a kan yanke hukunci shi kadai ba tare da tuntubarsu ba.
Waklinmu ya gano cewa, sau biyu ana dage taron kwamitin zartawar jam’iyyar ba tare da wani dalili ba a daidai wannan lokacin da ke fuskantar harkokin siyasa.
Sanarwa ta ce, “Shugaban Jam’iyyar yana yanke shawarar da ya ga dama shi kadai ba tare da tutubar kowa ba daga cikin mambobin kwamitn zartaswar, yana kuma jingina sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari don cimma wannan manufar tasa. Duk kokarin da muka yi na jawo hankalin shugaban jam’iyyar a kan wannan karya doka al’amarin ya ci tura.
“A kan haka muna kira ga shugaban jam’iyyar da ya gyara wannan lamari don a samu fahimtar juna, musamman ganin ana fuskantar harkokin siyasa ya kuma kamata jam’iyya ta hada kanta don samun nasara a zabukkan da ke gaba.” In ji sanarwar.
Haka kuma zaben fidda gwani da jam’iyyar ta yi a jihohi ya haifar da kura a wasu jihohin wanda in ba a yi gaggawar kai ceto ba jam’oiyyar na iya fuskantar matsala.
Wanne Hali Sauran Jam’iyyu Ke Ciki?
Masu lura da al’umurran yau da kullum sun bayyana cewa, yawancin ‘yan siyaasar da suka kasa samun nasarar cika burin su a zabukkan fidda da gwani da ke gabatarwa a halin yanzu akwai yiwuwar su koma wata jam’iyyar da suke ganin za su samu dammar cika burin na su. Kamar dai yadda ta faru da Peter Obi inda ya tattara ina shi ina shi ya fada jam’iyyar Labour Party (LP), ba tare da wani bata lokaci ba suka zabe shi a matsayin dan takarar shugabancin Nijeriya.
A taron da ya gudana a garin Asaba ya samu halartar wakilai 104 daga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja. Peter Obi ya samu nasara a kan abokan takararsa 3 (Farfesa Pat Utomi Misis Olubusola Emmanuel da Mista Joseph Faduri wadanda suka janye daga zaben) da kuri’u 96.
A jawabinsa bayan an sanar da nasarar lashe zaben, Obi ya yi alkawarin samar wa ‘yan Nijetiya cikakken tsaro da kuma ceto al’umma daga tsananin talauci da ake fuskanta a sassan Nijeriya.
Sauran ‘yan siyasa da suka samu nasarar zama ‘yan takarar jam’iyyunsu sun hada da Injiniya Rabiu Musa Kwankwanso wanda jam’iyyar NNPP ta tsayar da shi, Omoyele Sowore zai yi wa jam’iyyar AAC takara.
Haka kuma jam’iyyar PRP ta zabi Dakta Usman Bugaje a matsayin dan takararta, ya ce, da APC da PDP duk tafiyarsu daya, babu wanda yake da jadawalin ceto Nijeriya, a saboda haka yakamata ‘yan Nijeriya su yi kansu karatun ta natsu.