Shugabar majalissar dokokin kasar Angola, kuma mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar MPLA ta kasar Carolina Cerqueira, ta zanta da babban jami’i a ofishin siyasa, na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminis na birnin Beijing Yin Li.
Jami’an biyu sun gana ne a Juma’a a birnin Luanda fadar mulkin kasar Angola, albarkacin bikin raya al’adu da musayar harkokin yawon bude ido mai taken “Hello, Beijing”, wanda ke da nufin taimakawa mazauna birnin na Luanda, kara fahimtar muhimman abubuwan tarihi da na al’adun birnin Beijing, a matsayin sa na shahararren birni a kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp